Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu

Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu

  • Rikicin cikin gidan gwamnatin APC ya sake rurutawa inda aka fara fito fili ana ambaton sunaye
  • Kwanakin baya gwamnan jihar Kaduna yace akwai wasu yan tsiraru makusantan Buhari da basu son Tinubu yayi nasara
  • Yanzu mai magana da yawun Tinubu ya ce Ministan Shari'a makiyinsu ne kuma makiyin al'umma

Diraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mr Bayo Onanuga, ya sake caccakan makusantan Shugaba Buhari.

Onanuga ya bayyana Ministan Shari'a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami, a matsayin makiyi al'ummar Najeriya.

Ya kwatanta shi da Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mr Godwin Emefiele.

Malami
Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a dan gajeren tsokacin da yayi a shafinsa na Tuwita inda yake martani kan bukatar da Malami ya shigar kotun koli biyo bayan hukuncin da ta yanke ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan Takarar Gwamnan Kano Ya Cire Rai Tun Kafin a Gama Tattara Sakamako

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Abubakar Malami ma makiyi al'umma ne kamar Emefiele."

Sauya Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

A wani labarin kuwa, dokar canja fasalin kuɗi da Amfani dasu ta babban bankin Najeriya CBN zai kawo wa Sojoji tasgaro a ayyukan su.

Hakan ya fito daga bakin mai bawa shugaban ƙasa shawara akan harkokin tsaro NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai ritaya), yayin da ya bayyana a gaban wani kwamiti na majalisar wakilan tarayyar ranar Alhamis, rahoton Punch.

Monguno ya furta hakan ne ta bakin wakilin sa Adimiral Abubakar Mustapha.

Mustapha ya ce,

“Ba zan gushe ba, sai na ƙara da cewa, idan akai duba da tarayya ta duniya, za’a ga cewa, dokokin taƙaita zirga-zirgar kuɗi a hannun mutane da ire iren su da ake sakawa ba tare da an tauna an furzar ba, suna da matuƙar tasiri ga gudanar da harkokin gudanarwa ta sojoji, koda a ƙasashen da suka ci gaba ne."

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci Ta Darje Kujeru 2 Masu Tsoka, Ta Bukaci Tinubu Ya Ware Mata

"Saboda haka, idan ba’a auna ba aka sanya su, dole zasuyi wa harkokin sojoji illa, musamman ga gwarazan sojojin mu da aka tura wuraren da bazasu samu damar mallakar na’urorin da zasu biya ko amshi ƙudi ta manhajar kan waya ba."
"Hakan ka iya hana su biyan kuɗin kayan masarufi. Wannan shine babban maudu’in da mai bawa tsaron ƙasa akan harkar tsaro yake ta jan hankali akai.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel