Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Musanta Yin Murabus Daga PDP Duk da Ganin Wasika

Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Musanta Yin Murabus Daga PDP Duk da Ganin Wasika

  • Mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya karyata labarin da ke cewa ya fita daga jam'iyyar PDP mai mulki a jihar
  • A cewar hadiminsa, bai ma san da wasikar da ke yawo ba, inda yace yana nan daram a jam'iyyar ta PDP
  • An yada wata wasika a ranar Alhamis da ke nuna yadda mataimakin gwamnan ya fice daga PDP tare da bayyana dalilai

Manir Muhammad Dan Iya, mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya musanta yin murabus daga jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

Aminu Abubakar, daraktan yada labarai na mataimakin gwamnan ne ya fada wa jaridar TheCable ta wayar salula a ranar Alhamis 9 ga watan Faburairu, inda yace mai gidan nasa har yanzy mamba ne na PDP.

A wata wasikar da ta yadu a kafar sada zumunta a ranar Alhamis, an ga rubutun da ke cewa mataimakin gwamnan ya yi murabus daga PDP, ya tura wasikar ga shugaban jam'iyyar PDP na yankinsu.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu

Mataimakin gwamnan Sokoto ya karyata barin PDP
Mataimakin Gwamnan Sokoto Ya Musanta Yin Murabus Daga PDP Duk da Ganin Wasika | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bai san da wasikar da ke ta yawo ba

Abubakar ya kuma bayyana cewa, mataimakin gwamnan bai ma san da wasikar ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:
"Yanzu na yi magana da mai gida na.
“Ba gaskiya bane. Wasikar ba daga wurinsa ta fito ba. Bai sanya hannu a kanta ba. Har yanzu yana PDP."

Jita-jitan mataimakin gwamna ya bar PDP

A tun farko kun ji cewa, mataimakin gwamnan Sokoto, Manir Dan Iya ya fita daga jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

An ga wata wasika na yawo a kafar sada zumunta, inda aka ce mataimakin gwamnan ne ya rubuta don barin jam'iyyar ta PDP.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da zaben 2023 ke kara gabatowa a Najeriya, jam'iyyun kasar na ci gaba da ganin wani yanayi mai kama da musayar mambobi.

Uba sani ne dan takarar gwamnan APC a Kaduna

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Fitar da Matsaya a Kan Daga Zaben Shugaban kasa da ‘Yan Majalisa

A wani labarin kuma, kotun koli ta tabbatar da Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamnan APC da zai gwabza a zaben 2023.

Wannan na nufin kotun ta yi watsi da Sani Sha'aban, wanda ya shigar da karar neman a kwace tikitin Uba Sani har sau uku a kotu.

A tun farko, gwamna Nasir El-Rufai ya zabi Uba Sani a matsayin wanda yake so ya gaje shi a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.