Ba Mu Goyon Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya, In Ji NUT

Ba Mu Goyon Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya, In Ji NUT

  • Kungiyar malamai ta kasa NUT tace ba zata goyi bayan cire tallafin mai ba duba da irin wahalar da zai jefa mutane
  • Kungiyar ta bayyana haka ta bakin shugaban ta na kasa Titus Amba yayin taron su na shekarar 2023
  • Kungiyar ta kuma bayyana za su sanya kafar wando daya ga duk jihar da bata zartar da dokar mafi karancin albashi N30,000 ba

FCT, Abuja - Kungiyar malamai ta kasa a Najeriya (NUT) ta ce bata goyon bayan yunkurin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

Shugaban kungiyar na kasa Titus Amba, shi ne ya bayyana haka jiya Litinin a Abuja a wajen taron kungiyar na shekarar 2023, rahoton Daily Trust.

Fuel Scarcity
Ba Mu Goyon Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya, In Ji NUT. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Babban Magana: Kungiya Ta Bukaci Jami'an Tsaro Su Kama Shugaban INEC, Mahmoud Yakubu Kan Zaben 2023

Ya yi kira da a kara bibiyar tsarin tallafin ''da nufin kawar da cin hanci daga cikin tsarin.''

Gwamnatin tarayya ta ce za ta daina biyan kudin tallafin man fetur daga karshen watan Yuni bayan biyan naira tiriliyan 3.36 na tallafin tsahon wata shidan farko na shekarar nan.

Cire tallafin man fetur zai kawo wahala da kuncin rayuwa, Amba

Amma shugaban na NUT a jiya ya bayyana cewa tsadar man fetur da sauran abubuwan da suka shafi danyen mai ya janyo tsadar kayayyakin wanda ya jawo kunci ga dukkan masu neman kudi a kasar nan.

Amba ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta dau mataki kan duk jihar da bata zartar da dokar mafi karancin albashi N30,000 ga malaman makaranta ba.

Ya ce:

''Mun tattauna sosai da gwamnatocin jihohi kan batun mafi karancin albashi N30,000 , mun kuma shigar da korafe-korafe ga kungiyoyi game da wasu jihohi da basu bada hadin kai ba.''

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

Ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karin albashi ne ga iya malaman sakandire ba tare da yi wa malaman firamare karin ba.

Ya ce matsalolin tsaro, da suka janyo hare-hare a makarantu da garuruwa, sun yi sanadiyar mutuwar malamai da dalibai tare da lalata makarantu.

Ya roki gwamnati daga kowanne mataki da kuma masu ruwa da tsaki da su samar da tsaro ga makarantu da ma'aikatan ilimi.

Tinubu: Da zarar na ci zabe zan cire tallafin man fetur

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a 2023, ya ce da zarar ya ci zabe zai cire tallafin man fetur.

Ya sanar da hakan ne cikin takardar manufofinsa yana mai cewa cikin wata shida bayan aiwatar da dokar PIA zai cire tallafin don janyo hankalin masu zuba jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel