Karancin Naira ya sa Banki ya Caki ‘Yan N5 ya Cika Hannun Wani mutum

Karancin Naira ya sa Banki ya Caki ‘Yan N5 ya Cika Hannun Wani mutum

  • Wani dan Najeriya ya yada wani bidiyon lokacin da ya ciro damman N5 daga banki ya rike a hannunsa
  • A cewar mutumin, ya samo kudin ne daga wani bankin kasuwancin da yace bai samu manyan kudade ba
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar ciwon kai wajen nemo sabbin kudaden N200, N500 da N1000 da aka sauya kwanan nana

Wani dan Najeriya ya bayyana kukansa na rasa manyan kudi a bankunan Najeriya, inda aka bashi wasu kananan kudade.

A cewar mutumin, an bashi ‘yan N5 a banki kasancewar babu manya lokacin da ya je cire kudi a bankin kasuwanci.

A bidiyon da ya yada a TikTok ya nuna, mutumin ya bayyana kokensa kan yadda aka bashi ‘yan N5 a madadin manyan kudi.

AN ba dan Najeriya tarkacen 'yan N5 a banki
Karancin Naira ya sa Banki ya Caki ‘Yan N5 ya Cika Hannun Wani mutum | Hoto: TikTok/@storymustchange55.
Asali: UGC

Ba a dai san adadin kudin da ya cire ba, amma an ga dami takwas a hannunsa da suka cika fal.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan ‘Yahoo Suka Damfari Tsohuwa, Suka Sace Duka Dukiyar da ta Mallaka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa, bankinsa ya bashi kudin ne alamar da ke nuna babu sabbin kudade ko wasu manya.

‘Yan Najeriya dai na ci gaba da fama da karancin sabbin N200, N500 da N1,000 a bankunan Najeriya.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

@Egbe Adebukola:

"Lallai ke mai arziki ce.”

@ARTHUR:

"Rayuwa ta fara sauki yanzu kam.”

@Ifeyinwa Eucharia Uyanneh:

"Wannan ai horo ne.”

@hammed Aminat:

"Ya kamata ka gode Allah ma ka ga N5 din har ka karba.”

@ADUNNI ADE:

"Naira 5 a yanzu dai ya samu daraja, ba zan cire rai ba.”

@user9973819636447:

"Malam kana bukata ne shi yasa ka karba to meye na korafi?”

@Ojuolape Oloyede:

"A kalla dai kana da tsabar kudi a hannu.”

A halin da ake ciki, 'yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da yadda babban bankin CBN ya kawo batun sauyin kudi a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Na kusa da Tinubu ya tona asiri, gwamnan CBN na da mugun nufi kan 'yan Najeriya

Mutanen kauye za su rufe kasuwa

A wani labarin, kun ji yadda wasu mazauna jihar Kebbi suka bayyana aniyar rufe kasuwancinsu saboda karancin sabbin kudade a kasar.

Wannan na zuwa bayan da gwamnatin Buhari ta ce za a daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 tare da maye gurbinsu da sabbi.

Babban abin da ake maida hankali a kai a Najeriya a yanzu shine yadda bankuna ke karancin sabbin kudaden.

Asali: Legit.ng

Online view pixel