Mun Gaza Gudanar da Kasuwancinmu, Za Mu Rufe Kasuwa Kowa Ma Ya Huta, Inji ’Yan Kasuwa a Kebbi

Mun Gaza Gudanar da Kasuwancinmu, Za Mu Rufe Kasuwa Kowa Ma Ya Huta, Inji ’Yan Kasuwa a Kebbi

  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da sabbin kudi da kuma yadda karancinsu ke shafar kasuwancinsu
  • ‘Yan kasuwa a jihar Kebbi sun bayyana yunkurin rufe kasuwanci saboda kwata-kwata ba sa samun ciniki yadda ya kamata
  • ‘Yan kasa da yawa sun ziyarci bankuna don cire kudi, amma lamarin ya ci tura, domin babu kudaden bankuna da yawa

Birnin Kebbi, jihar Kebbi - ‘Yan kasuwa a Birnin Kebbi sun yanke shawarin rufe kasuwa gaba daya saboda yadda karancin sabbin Naira ke hana su yin harkokinsu na yau da kullum.

Shugabana kungiyar ‘yan kasuwa jihar Kebbi, Alhaji Umar Dangura Gwadangwaji ne ya bayyana hakan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, ‘yan kasuwa sun yi duk wani kokarin samun sabbin kudi daga bankunan kasar nan amma hakan ya gagara.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addinin Kirista Ya Fada Wa Yan Najeriya Irin Yan Takarar Da Zama Dole A Kauracewa

Yadda 'yan kasuwa ke kokawa game dakarancin Naira a Kebbi
Mun Gaza Gudanar da Kasuwancinmu, Za Mu Rufe Kasuwanni Kowa Ma Ya Huta, Inji ’Yan Kasuwa a Kebbi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake jawabi game da ci gaba da karbar tsoffin kudade, ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Idan muka ci gaba da karba daga hannun kwastomomi, wane banki ne zai karba daga wurinmu bayan karewar wa’adi."

Masu kayan abinci da direbobi sun daina karbar tsoffin kudi

A rahoton majiya, direbobi da masu sana’ar siyar da abinci a Birnin Kebbi sun daina karbar tsoffin kudade tun ranar Talata daga hannun kwastomomi.

Hakan ya faru ne saboda bankuna da masu POS a birnin sun gaza ba da sabbin Naira da aka ce sun fara yawo tun watan jiya.

A cewar rahoton, mutane da yawa ne suka bi layin ATM na tsawon awanni, amma sun gaza samun kudin cikin sauki ko rasa su ma kwata-kwata.

Ina neman sabbin kudi zan siya abinci, abu ya gagara

Yusuf Ali, wani kwastoman bankin GTB ya koka da cewa:

Kara karanta wannan

Sabbin Kudi: Mutanen Karkara Wa'adin CBN Zai Wa Illa, El-Rufai

“Tun ranar Litinin nake zuwa banki din na cire kudi saboda na siya kayayyakin abinci ga iyalaina saboda babu wanda ke karbar tsoffin kudi. Amma lamarin na kara dagulewa saboda ban samu kudin a ATM ba.
“Kalli yadda nake rike da kudade jingim amma babu mai karbarsu daga wurina saboda tsoffi ne kuma ban sami sabbin daga bankuna ba.”

Masu POS na karbar tsoffin kudi, amma sun kara caji

Legit.ng Hausa ta tattauna da wasu 'yan mata da ke siyar da abincin karin kumallo a bakin tsohuwar kasuwa da ke jihar Gombe don jin yadda kasuwar tasu ke tafiya.

A cewar Khadija Abubakar, mai siyar da tuwo:

"Ka ga yanzu ma ina da tsoffin kudi, kuma ina karba. Mai POS din unguwarmu yana karba, jiya ma na kai masa N15,000. Amma a duk N1000, sukan karbi N100. Kenan N1500 na bayar jiya aka saka min N15,000 a akant."

Wata mai shagon siyar da waina, Maimuna Umar cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Sokoto: Jama'a Sun Rude Bayan 'yan Kasuwa Sun Daina Karbar Tsofaffin Kudi

"Ina jin dar-dar, amma ina karbar tsofaffin kudade. Ina da kani mai aiki a banki, da sana'ar nan na dauki nauyinsa, don haka yana kai min kudade na. Ka ga cinikinmu a rana yana fin N50,000, ya za mu yi idan muka daina karba? Idan wa'adi ya wuce dai mun daina, amma yanzu muna karba."

Majalisa za ta zauna da shugabannin bankuna

A wani labarin kuma, kunji yadda majalisar dokoki a Najeriya ta bayyana bukatar zama da shugabannin bankuna a kasar.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi a bankuna.

CBN a baya ya ce, akwai kudi a kasa, bankuna sun ki zuwa su dauka don rabawa 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel