Har Yanzu Buhari Bai Yi Magana Kan Kisan Fulani Da Bam Ba, Allah Wadai Wallahi: Miyetti Allah

Har Yanzu Buhari Bai Yi Magana Kan Kisan Fulani Da Bam Ba, Allah Wadai Wallahi: Miyetti Allah

  • Miyetti Allah ta yi Alla-wadai da rashin maganar Shugaba Buhari har yanzu game da kisan Fulani da Bam a Nasarawa
  • Kungiyar tace gwamnatin tarayya ko uffin bata ce ballantana kafa kwamitin gudanar da bincike
  • Bam ya hallaka makiyaya sama da 40 da suka tafi jihar Benue karban Shanunsu da aka kwace

Kungiyar kare hakkin makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN ta bayyana takaicinta game da shirun gwamnatin tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari kan harin Bam din da ya hallaka Fulani Makiyaya 40 a jihar Nasarawa.

Kakakin kungiyar Miyetti Allah, Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa wannan kisan gilla aka yiwa al'ummarsu kuma wajibi a gudanar da bincike kan yadda Bam ya tashi da su, rahoton TheCable.

A jawabin da yayi, yace:

"Ko ba komai, ya kamata Shugaban kasa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan ta'addanci."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ganduje ya Bayyanawa Buhari Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

"Abin kunya ne cewa yayinda aka kashe mutane, shugaban kasa na can jihar Katsina na shan walima."
Miettt
Har Yanzu Buhari Bai Yi Magana Kan Kisan Fulani Da Bam Ba, Allah Wadai Wallahi: Miyetti Allah
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kwato mana hakkinmu

Abdullahi ya kara da cewa:

"Muna kira ga hukumar kare hakkin dan adam ta gudanar da bincike kan wannan lamari da kuma kashe-kashen da Sojin sama ke yi a Nasarawa."
"Wadannan makiyayan da aka kashe yan Najeriya ne, suna da hakki kaman ko wani dan Najeriya saboda haka wajibi ne doka ta kare su."
"Rashin rai guda daya ya isa takaici ballantana rashin mutum 40 lokaci guda."

Kawo yanzu mutum 37 muka birne: Gwamnan Nasarawa ya bayyana

An yi jana'izar Fulani Makiyaya da mahauta 37 da Bam ya hallaka a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana hakan a jawabin da yayi a shirin 'Politics Today' na tashar ChannelsTV da yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

Yace:

"Mun birne mutum 37 jiya, ina da wannan tabbaci. Takwara na jihar Benue ya ce suma sun birne mutane a jiharsu."
"Mutum tara cikin yan gida daya ne. Fulanin jihar Nasarawa, kuma mahaifinsu ya zo na yi masa ta'aziyya."

Kungiyar kare hakkin makiyaya a Najeriya watau Miyetti Allah (MACBAN) ta tuhumci hukumar sojin saman Najeriya da kashe wadannan Fulani Makiyaya.

Shugaban MACBAN, Baba Othman Ngelzarma, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar, rahoton

Asali: Legit.ng

Online view pixel