Ganduje Ya Ziyarci Buhari, Ya Bayyana Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

Ganduje Ya Ziyarci Buhari, Ya Bayyana Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa Kano a shirye ta ke don karbar Shugaba Buhari a ziyarar da zai kai
  • Gwamnan ya bayyana cewa, ya kwashi wakilan jihar inda suka ziyarci Buhari don godiya kan koken jama’a da ya ji har aka dage wa’adin daina karbar tsofaffin kudi
  • Gwamnan ya ce akwai manyan ayyuka da zasu kaddamar da suka hada da na tarayya da na jiha wanda Kano tana shirye don karbarsa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yace jihar a shirye ta ke don karbar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari da Ganduje
Ganduje Ya Ziyarci Buhari, Ya Bayyana Matsayar Kanawa Kan Ziyarar da Zai Kai Jihar. Hoto daga @Buharisallau
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, ya sanar da hakan a ranar Lahadi yayin jawabi ga manema labarai bayan ganawa da Buhari da yayi a Katsina.

“A matukar shirye mu ke don karbarsa kuma akwai abubuwa da yawa da zai kaddamar har da ayyukan gwamnatin tarayya da na jiha.”

Kara karanta wannan

Duk Da Rashin Amincewar Ganduje, Buhari Zai Kai Ziyara Jihar Kano a Gobe Litinin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Ganduje yace.

Sa’o’i kadan a baya, jihar ta rubuta wasika ga shugaban kasa domin neman dage ziyarar sakamakon halin da jihar ta shiga sakamakon wa’adin da aka saka na rufe canza kudi.

Sai dai, babban bankin Najeriya yanzu ya tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin kudi har zuwa 10 ga watan Fabrairun 2023.

A yayin jawabi a ranar Lahadi, Ganduje yace jihar ta gamsu da martanin shugaban kasan kan damuwa da ‘yan kasa suka shiga.

“Gani ya kori ji. Kuna ganin na jagoranci wakilai daga jihar Kano kan batun sabbin takardun Naira kuma mun ga shugaban kasa.”

- Yace.

“Mun mika korafe-korafen jama’ar Kano kuma muna matukar farin ciki. Yayi mana bayani tare da tabbatar mana da cewa ya tsawaita wa’adin tare da kara yawan sabbin takardun kudi ta yadda wahalar talaka za ta ragu.
“Mun sanar masa da cewa Kano ce jiha mafi yawan mutane kuma cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya, ta biyu bayan Legas.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

“Amma a bangaren hada-hadar tsabar kudi, Kano tana gaba da Legas saboda Legas ta yi nisa a daina amfani da tsabar kudi.
“Amma Kano kauye ce idan aka alakanta. Toh duk da haka muna da kananan hukumomi 24 da basu da bankuna. Da yamma bankunan jihar suna kwaryar birnin Kano.
“Toh ga gwada wahalar kauyuka, jama’ar kauye da hada-hadar kudin da ba tsaba ba. Amma muna farin ciki da tsawaita wa’adin da yawan takardun kudin.
“Toh, muna godiya ga shugaban kasa kan kokarinsa.”

Katsinawa sun balle zanga-zanga bayan ziyarar Buhari

A wani labari na daban, fusatattun matasan Katsina sun balle zanga-zanga da kone-kone a titin da Buhari ya kaddamar.

Sun yi hakan ne don kokawa kan matsin rayuwa da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel