An Yi Jana'izar Fulani 37 Da Bam Ya Kashe a Jihar Nasarawa, Gwamna Abdullahi Sule

An Yi Jana'izar Fulani 37 Da Bam Ya Kashe a Jihar Nasarawa, Gwamna Abdullahi Sule

  • An birne kimanin mutum arba'in sakamakon harin Bam da aka kai kan Fulani Makiyaya a jihar Nasarawa
  • Gwamnan jihar ya tabbatar da cewa kawo yanzu an birne mutum 38 kuma akwai saura a Benue
  • Kungiyar Miyetti Allah ta ce jami'an sojojin Najeriya ne suka kai wannan mumunan hari kan mutane bai gaira ba dalili

Nasarawa - An yi jana'izar Fulani Makiyaya da mahauta 37 da Bam ya hallaka a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana hakan a jawabin da yayi a shirin 'Politics Today' na tashar ChannelsTV da yammacin Alhamis.

Yace:

"Mun birne mutum 37 jiya, ina da wannan tabbaci. Takwara na jihar Benue ya ce suma sun birne mutane a jiharsu."
"Mutum tara cikin yan gida daya ne. Fulanin jihar Nasarawa, kuma mahaifinsu ya zo na yi masa ta'aziyya."

Kara karanta wannan

Har Yanzu Buhari Bai Yi Magana Kan Kisan Fulani Da Bam Ba, Allah Wadai Wallahi: Miyetti Allah

Jana'iza
An Yi Jana'izar Fulani 37 Da Bam Ya Kashe a Jihar Nasarawa, Gwamna Abdullahi Sule Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji ne suka kashe mana yan'uwa, Miyetti Allah

Kungiyar kare hakkin makiyaya a Najeriya watau Miyetti Allah (MACBAN) ta tuhumci hukumar sojin saman Najeriya da kashe wadannan Fulani Makiyaya.

Shugaban MACBAN, Baba Othman Ngelzarma, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar, rahoton SaharaReporters.

Ya ce makiyaya kimanin 30 aka kashe kuma dakarun sojin saman Najeriya dake Makurdi ne suka kashe su.

Ngelzarma
Jami'an Sojin Najeriya Ne Suka Kashe Fulani Makiyaya 28 da Bam, Miyetti Allah Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

Jawabin Miyetti Allah

A cewar jawabin:

"Kungiyar Miyetti Allah MACBAN tayi Allah-wadai da kisan makiyaya 30 da dabbobinsu da wani harin Bam yayi a ranar 21 ga Junairu 2023 a garin Rukubi, karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa."
"Wadanda aka kashe sun tafi Makurdi ne amsan shanunsu 1,250 da jami'an gandun dajin jihar Benue bayan biyan taron 29 Million Naira."
"Bayan biyan kudin taran, makiyayan suka hau mota daga Makurdi... kuma yayin sauya shanun dake motoci ne aka kai musu hari wanda ya kashe makiyaya 31, mahauta Hausawa 8 daga Benue da suka rakasu don tayasu sauke shanun kuma mutum 4 na asibiti yanzu a Lafia."

Kara karanta wannan

Gwamna Sule: Jajiberin 'Dana Zai Rasu, Na Dinga Rarrashin Mahaifin da ya Rasa Yara 9 da Shanu 70 a Tashin Bam din Nasarawa

"Wannan shine karo na uku da wannan abun zai faru. A lokuta biyu na farko, ya bayyana karara cewa jami'an sojin saman Najeriya na da hannu wajen kora shanun mutane a iyakan Benue da Nasarawa."
"Bayanan da muka samu sun nuna cewa wadanda suka kai wannan hari sun samu labarin cewa an karbo shanun daga wajen jami'an gandun dajin Benue don cin zarafin Makiyaya da dukiyarsu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel