Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Dr Sani Rijiyar Lemo

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Dr Sani Rijiyar Lemo

Biyo bayan kalamai da suka yawaita kan lamarin sauya fasalin takardun Naira da kuma daina amfani da tsaffin, shugaban cibiyar CICID dake jami'ar Bayero dake jihar Kano, Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya yi nasa kira ga gwamnati.

A jawabin da ya fitar ranar Lahadi, 28 ga Junairu, 2023 ya bayyana cewa shugabanci na kwarai kullum sauki yake nemawa mutane ba tsanani ba.

Karanta jawabansa a nan:

Dr Sani
Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Dr Sani Rijiyar Lemo Hoto: Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
Asali: Facebook

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma

1. Allah (SWT) yakan zo da abubuwa masu dadi da marasa dadi a rayuwa, don su zamanto jarraba wa ga bayinsa, domin ya bayyana wadanda suka fi kyautata ayyukansu. Wajibi ne ga duk wani Musulmi ya rika halarto da wannan ma’ana a zuciyarsa duk sanda ya ga an shiga wani yanayi bako a rayuwa. Ya yi kuma kokarin cinye wannan jarrabawa.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Hukumar samar da takardun kudade karkashin babban bankin Kasa, tare da sahhalewar Shugaban Kasa sun yi tunanin sake fasalin wasu takardun kudaden Nigeria domin wasu maslahohi da suka hango da kuma magance wasu matsaloli. Muna musu kyakkyawan zato cikin wannan kuduri nasu, muna kuma fatan a yi nasara cikin hakan.

3. Amma duk da haka, wajen tabbatar da waccan kyakkyawar manufa, talakawa a Nigeria, sun shiga wani mawuyacin hali kuma mai ban tausayi, musamman a kauyukanmu na Arewa. Don haka muna rokon hukumar da wannan abu ya shafa da su duba halin da Jama’a suke ciki, su amsa kiraye-kirayen al’umma na kara wa’adin da suka saka na dakatar karbar tsofaffin kudi, ko kuma su yi wa tsarin gyaran fuska, don fitar da al’umma daga wannan kangi mawuyaci.

4. Shugabanci na kwarai har koyaushe yana aikata abin da zai saukakewa al’umma rayuwarsu ne ta yau da kullum, da kuma sama musu walawala a harkokinsu, da guje wa jefa su cikin tsanani da wahalhalu.

Kara karanta wannan

Sai Yanzu Ka San Za Ka Zagi Buhari?, Atiku Ya Caccaki Tinubu

5. Fatanmu hukuma za ta dubi wannan lamari ta kuma yi abin da ya dace. Allah ya musu kyakkyawan jagoranci, ya ba mu zamanan lafiya da arzuki mai dorewa a Kasarmu. Amin.

Muhammad Sani Umar

Doha- Qatar

January, 28th, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel