Kano: An Gano Asibitoci Da Shagunan Sayar Da Magunguna 130 Da Likitocin Bogi Suke Bude Suna Aiki

Kano: An Gano Asibitoci Da Shagunan Sayar Da Magunguna 130 Da Likitocin Bogi Suke Bude Suna Aiki

  • Wata kwamitin bincike da aka kafa a karamar hukumar Tudun Wada a Kano ta ce ta gano asibitocin bogi da shagon magunguna 130
  • Kwamitin ta ce daga cikin masu tafiyar da asibitocin har da wani injiniyar lantarki da wani wanda sakandare kawai ya gama
  • Daga cikin likitocin bogin da aka kama har da wani da ya yi wa wata mata karin jini da jinin mai kanjamau a lokacin da ta zo maganin zazabin cizon sauro

Wata kwamiti a karamar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, ta bayyana cewa ta gano asibitoci da shagunan sayar da magunguna 130 da likitocin bogi ke tafiyar da su, wasu na takardan sakandare gare su, The Punch ta rahoto.

Taswirar Jihar Kano
Kano: An Gano Asibitoci Da Shagunan Sayar Da Magunguna 130 Da Likitocin Bogi Suke Bude Suna Aiki. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kwamitin wacce shugaban karamar hukumar, Alhaji Tijjani Matata, ya kafa ta ce yayin bincikenta ta gano daya cikin likitocin injiniya ne da lantarki wanda ke da asibiti mai gado takwas da ya yi ikirarin yana maganin kowanne ciwo, Koko TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Daga Rabon Fada, An Sokawa Matashi Wuka a Hannu, Yanzu An Yanke Hannun Baki Daya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikinsu akwai wani da ya saka wa wata mata jinin mai kanjamau yayin da ta zo maganin zazabi

Ciyaman din kwamitin, Alhaji Abubakar Karafe kuma ya fada wa manema labarai cewa daya daga cikin likitocin bogin ya saka wa wata mata jini mai cutar kanjamau lokacin da ta zo yin maganin zazabin cizon sauro.

Karafe ya ce:

"Abin takaici ne yadda muka gano injiniya na lantarki yana tafiyar da asibiti mai zaman kanta yana ganin marasa lafiya yana rubuta magani, yana karin ruwa, jini, har yana kulawa da masu ciki. Daya cikinsu ya saka wa wata mata ciki mai HIV.
"Mun gano wani mai maganin gargajiya, amma yana kwantar da masu kwalera. Mun kwashe su mun kai su asibiti mai kyau. Mafi yawancinsu ba su san komai game da kiwon lafiya ba.
"Daya cikinsu ya ce shi malamin jinya ne amma muka gano satifiket din sakandare kawai gare shi."

Kara karanta wannan

"Ba Zan Hakura Ba" Gwamnan Arewa Da Aka Yi Wa Ruwan Duwatsu Ya Magantu

Karafe ya kara da cewa sunyi binciken ne bayan korafe-korafe da dama da suka samu daga mazauna yankin kan karuwar asibitoci masu zaman kansu da shagunan magani a kauyukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel