Gwamna Tambuwal Ya Sha Alwashin Hukunta Masu Hannu a Harin Ayarinsa

Gwamna Tambuwal Ya Sha Alwashin Hukunta Masu Hannu a Harin Ayarinsa

  • Gwamnan Jihar Sakkwato ya yi Alla-Wadai da harin da wasu 'yan daba suka kai wa Ayarinsa ranar Lahadi a Wamakko
  • Gwamna Tambuwal ya ce tuni aka gudanar da bincike kan lamarin kuma an kama wasu daga cikin maharan
  • Kwamishinan yada labarai na jihar ya ce maharan sun lalata wasu motoci yayin harin

Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya sha alwashin zakulo duk masu hannu a harin da aka kaiwa ayarinsa ranar Lahadi domin doka ta yi aiki a kansu.

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda wasu 'yan daba suka yi ruwan duwatsu kan Ayarin gwamnan yayin da suke hanyar komawa daga wurin kamfe.

Gwamna Aminu Tambuwal
Gwamna Tambuwal Ya Sha Alwashin Hukunta Masu Hannu a Harin Ayarinsa Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Twitter

Punch ta ce Lamarin dai ya faru ne sa'ilin da gwamna da yan tawagarsa ke hanyar komawa daga wurin gangamin kamfen PDP da aka gudanar a kananan hukumomin Silame da Wamakko.

Daga cikin manyan mutanen dake Ayarin har da 'yan takarar gwamna a Sakkwato da Kebbi karkashin inuwar PDP, Mallam Saidu Umar da Janar Aminu Bade da sauyan manyan jiga-jigan siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki hukumomi ke shirin dauka?

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da masu ruwa da tsaki da masu rike da mukaman siyasa, Tambuwal yace tuni aka yi ram da wasu daga cikin maharan.

Tribune Online ta rahoto Tambuwal na cewa:

"Abun takaici ne muna hanyar dawowa daga Wamakko ranar Lahadi, a daidai ofishin Aliyu Magatakardan Wamakko, wasu 'yan daba suka farmaki Ayarina zamu gidan gwamnati."
"Ba zamu lamurci kowace kalar iskancin rikici ba a jihar Sakkwato, ba zamu yarda a yi wasa da zaman lafiyarmu ba. Ina kira da manyan siyasa su guji ta da yamutsi, su umarci magoya bayansu da yin kamfe mai tsafta."

"Kamar yadda kowa ya sani muna son zaman lafiya kuma muna ta nanata kokarin samun dawwamammen zaman lafiya a Sakkwato ba tare da duba banbance-banbance ba."

Game da wannan batu, kwamishinan yada labarai na jihar, Akibu Dalhatu, yace jagoran kai harin mai suna Abu, wanda dama dakarun Sibil Defens na nemansa ya shiga hannu.

Yace maharan sun lalata wasu motoci daga cikin Ayarin mai girma gwamna kuma sun yi awon gaba da Babura biyar a wurin taron kamfe a Wamakko.

Atiku Zai Bude Boda Idan Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Tambuwal

A wani.labarin kuma Gwamna Tambuwal ya ce da zaran Atiku Abubakar ya ci zabe zai bude iyakokin Najeriya

Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar kuma gwamnan Sakkwato ya faɗi wasu muhimman ayyuka da PDP xata yi idan ta kwace mulki a 2023.

Gwamnan ya kuma tausaya wa al'ummar jiharsa bisa fama da hare-haren yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel