Mutane 7 da Zasu iya Canza Fasalin Najeriya a Shekarar 2023

Mutane 7 da Zasu iya Canza Fasalin Najeriya a Shekarar 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu jiga-jigai shida na kasar ne ake ganin zasu iya canza akalar kasar a wannan shekarar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan shekarar za ta tarbi sabon shugaban kasa yayin da shugaba Buhari zai yi bankwana a ranar 29 ga watan Mayu daga barin mulkin da ya zarce.

Dama, 'yan takara 18 ne za su fafata a zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu. Wanda daya daga cikinsu ne zai karba mulkin kasar a ranar 29 ga watan Mayu.

Ana sa ran samun sabbin 'yan majalisa. Zaben 'yan majalisun tarayyan zai gudana ne a rana daya da na shugaban kasa.

Zaben gwamanoni zai gudana a jihohi 30 cikin 36 a ranar 11 ga watan Maris. Zaben jihar Kogi, Bayelsa, Edo, Ondo, Ekiti da Osun za a gudanar da su a lokuta daban-daban.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige Buhari da Tirka-Tirka 10 da Aka Yi a Majalisar Tarayya a Shekarar 2022

Shekarar 2023
Mutane 7 da Zasu iya Canza Fasalin Najeriya a Shekarar 2023. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Buhari

An zabesa a shekarar 2015 a matsayin shugaban kasa na 15, matakan Buhari za su saisaita shekarar.

Duk da ya bawa 'yan Najeriya tabbacin zai bada gudunmawar ta hanyar tabbatar da an gudunar da zaben mai ban sha'awa tare da ba hukumar zaben damar shirya zaben yadda ya dace, kowa ya sanya ido don ganin ya cika alkawuran.

"INEC a shirye take saboda na tabbatar da an basu kayan aikin da suka bukata saboda ba na son wani uzurori cewa gwamnati ta hanasu kudi."

- A cewar Buhari yayin amsa tambaya game da shirin INEC don aiwatar da zaben a Washington DC, USA a wata zantawa.

Masu hasashe sun yi imanin cewa idan har shugaban kasa ya cika alkawarinsa, dimokaradiyyar kasar za ta karfafa kuma burin 'yan Najeriya zai bunkasa.

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

2. Shugaban INEC, Yakubu

Shugaban hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yukubu, shima ana sa rai a kansa duba da yadda yake hangen nesa kuma yana bada umarni game da yadda za a shirya a rumfunan zabe zuwa ga kwamishinonin hukumar na kasa wadanda sune ke da alhakin duba kwamishinonin zaben na yankuna a fadin jihohi.

Nasara ko akasin haka na zaben gaba daya na kafadun Yakubu. Shugaban aiwatar zaben, aikinsa ne ya tabbatar zaben ya guduna ba tare da dogaro da kowa ba. Ana sa ran hukumar, wacce take karkashinsa ta nuna gaskiya a lamurranta da kuma mu'amalarta da sauran masu rike da mukamai.

Yakubu ne zai ayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan sanar da sakamakon da shugabannin yankuna suka kawo, wanda dama farfesa ne a daya daga cikin jami'o'in kasar.

3. IGP Baba

Sifeta-janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, na da alhakin shirya 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Fitattun Yan Najeriya a Turai Sun Daukar Wa Atiku Gagarumin Alkawari Gabannin 2023

Baya ga rumfunan zabe, kasar na cigaba da fuskantar rikice-rikicen da suka shafi zabe. Mutane da dama sun rasa rayukansu da wadanda suka samu raunuka ba adadi a karo daban-daban.

Ana sa ran sifeta-janar na 'yan sanda, ya nuna dogaro da kai ba tare da bangaranci ba.

4. CJN, Ariwoola

Shugaban Alkalan Najeriya (CJIN), Alkali Olukayode Ariwoola, na kotun koli, babbar kotun Najeriya da take yanke hukunci na karshe.

Duk wasu rikice-rikicen zaben idan suka yi kamari za su kare ne a kotun kolin.

Kafin zaben, CJN a ranar 7 ga watan Nuwamba, ya rantsar da mambobin sauraron karar zaben 2023. Alkalai guda 307 da zasu saurara gami da kawo maslaha kan rikicin da ka iya tasowa daga zaben 2023.

"A matsayina na shugaban Alkalan Najeriya, ba zan lamunci kowanne irin ganganci, murdiya da rikicin al'umma ba."

Mista Ariwoola yayi jan kunne ga jami'an shari'a da za su saurara shari'ar bayan zabe.

Kara karanta wannan

Za a Fara Haska Shiri Kan Rayuwa da Falsafar Shugaba Muhammadu Buhari Ranar Farko ta Sabuwar Shekara

5. Wanda zai lashe zaben shugaban kasa

Wanda zai lashe zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu zai taka mihimmiyar rawa wajen gyara kasar wannan shekarar.

Dukkan 'yan takarar 18 sun nuna son gadar mulkin daga shugaba Muhammadu Buhari a 29 ga watan Mayun wannan shekarar, amma manuniya na nuna 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; na PDP, Atiku Abubakar; na LP, Peter Obi; da Rabi'u Musa Kwankwaso a NNPP. Masu kada kuri'u 84 miliyan ne zasu tabbatar da makomar wadannan 'yan takarar a rumfunan zabe 176,846 dake fadin kasar.

Bayan rantsarwa, sabon shugaban kasar zai karbi ragamar kasar, ya bada mukamai, duk da sakataren gwamnatin tarayya (SFF), shugaban ma'aikata da hadimansa.

6. Aliko Dangote

Aliko Dangote shi ne bakar fatar da yafi kowa kudi kuma shi ne mutum na 75 da yafi kowa kudi a duniya, kamar yadda Bloomberg Billionaire ta kididdiga. Shi ne shugaba kuma mamallakin kamfanonin Dangote, masana'antar da tafi kowacce girma a yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

Bayan Shakaru Takwas, Za'a Rataye Sagir Wada, Wanda Ya Yi Gunduwa-Gunduwa da Kishiyar Mamarsa a Kano

A watan Oktoba, 2022, hukumar tacewa da gyara man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta bayyana yadda matatar man fetur na Dangote ke kashi na 97 wajen kammala. Kuma ana sa ran zai fara samar da fetur a wannan shekarar.

Matatar, wacce ke iya tace ganguna 650,000 a rana, ana sa ran zai cika sharuddan kasar na samar da kayayyakin man fetur.

7. NPC, Isa-Kwarra

Yanzu da shekaru sha bakwai suka shude, kasar na shirye-shiryen tsara kidaya. An yi kidayar karshe ne a 2006 yayin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo.

Ya kamata a ce ana yin ta duk bayan shekaru 10, amma yanzu an shirya yi a watan Afirilun wannan shekarar. An koya yadda za a gudanar da kidayar a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Daily Trust a ranar Lahadi ta ruwaito yadda za a aiwatar da kidayar karkashin jagorancin Nasir Isa-Kwarra. Kowa ya zura masa na mujiya don ganin ya za a gudanar da aikin.

Masana sun ce mahimmancin kidayar ba abun rainawa bane saboda shi ne zai taimaka wajen shirya ayyuka, kuma babu wani cigaba da zai bada ma'ana ba tare da aiwatar da kidaya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel