Za a Fara Haska Fim Kan Rayuwar Shugaba Buhari da Falsafarsa a Ranar 1 ga Janairu

Za a Fara Haska Fim Kan Rayuwar Shugaba Buhari da Falsafarsa a Ranar 1 ga Janairu

  • A ranar 1 ga watan Janairun 2023, za a haska fim kan rayuwa da falsafar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Kamar yadda Malam Garba Shehu ya bayyana, za a haska fim din gidajen talabijin na Channels TV, NTA da TVC duk a ranar sabuwar shekarar
  • Fim din zai haska shugaban kasan har da wasu 'yan uwa da abokansa wadanda zasu bada bayani kan rayuwarsa kacokan

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa, ta ce za a fara haska fim din rayuwar shugaba Muhammadu Buhari da falsafarsa daga ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana hakan a wata takardar da ya fitar ranar Asabar.

Baba Buhari
Za a Fara Haska Fim Kan Rayuwar Shugaba Buhari da Falsafarsa a Ranar 1 ga Janairu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shehu ya ce shirin na tsawon sa’a daya mai suna ‘Essential Muhammadu Buhari’ za a fara nuna shi a gidajen talabijin na TVC, Channels TV da NTA a ranar 1 ga watan Janairu da karfe 4:30 na yammaci da karfe 6 na yamma da kuma karfe 8 na yammacin ranar.

Kara karanta wannan

A Ranar Aikin Karshe a Shekarar 2022, Buhari Ya Fitar da Sababbin Mukamai 9

Fim din ya tattaro "hankali, rayuwa da falsafar" shugaban kasan da aka gabatar "ta hanyar maganganunsa, da kuma wasu 'yan uwa, abokai da abokan tarayya".

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Essential Muhammadu Buhari," shiri ne na tsawon sa'a daya game da Shugaba Muhammadu Buhari, tunaninsa, rayuwarsa da falsafarsa za su fara nunawa a talabijin da YouTube.
"Hoton fim ne na Shugaban kasa ya fada a cikin kalamansa, da kuma bakin wasu cikin ‘yan uwa, abokai da abokan huldarsa.”

- In ji sanarwar.

Sauran tashoshin talabijin da za su nuna shirin sun haɗa da Arise TV a ranar 2 ga watan Janairu da ƙarfe 5 na yamma sai kuma ƙarfe 6 na yamma a kan Trust TV a wannan rana.

AIT kuma za ta nuna fim din a ranar 2 ga Janairu da karfe 8 na dare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Jaridar TheCable ta ruwaito wani faifan bidiyo daga fim din inda Buhari ya bayyana cewa bai ga abin dariya da “Jubril na Sudan” ba da aka kira shi da shi ba.

A shekarar 2017, wani shirin fim mai suna ‘The Human Side of President Buhari’ ya fito a gidan talabijin.

Bidiyon mai tsawon mintuna hamsin da biyar, wanda sashen yada labarai na fadar gwamnatin jihar suka hada, ya samu ministoci da hadiman shugaban kasa da sauran mambibin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun bayyana ra’ayoyinsu kan salon tafiyar Buhari, da turbar masu ba da shawara, da sauran su.

Buhari yayi shagalin Kirsimeti a Abuja

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi shagalin bikin Kirsimeti da mazauna babban birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel