Dirama, Karamin Yaro Ya Murtuke Fuska, Ya Nemi a Ba shi Abinci a Baki

Dirama, Karamin Yaro Ya Murtuke Fuska, Ya Nemi a Ba shi Abinci a Baki

  • Wani karamin yaro ya ja hankalin mutane da dama a Soshiyal midiya da wasu halaye masu ban dariya sa'ilin da aka zuba masa abinci
  • A bidiyon wanda Trobeni ta wallafa, yaron ya yi watsi da abincin ya nemi a kawar da shi tare da nuna kamar yana cikin aiki
  • Har sai da wanda ta kai masa abinda ta tsuguna ta ba shi a baki sannan ya yarda ya ci abincin a wani bidiyo

Masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani sun nishadantu da Bidiyon wani karamin yaro mai ban dariya, wanda ya nuna yana wani abu ne lokacin da aka mika masa abinci.

Karamin yaron wanda ya dafi wayar salula ya murtuke fuska tamkar wani Oga ya hakince a kujera ya nuna ko kaɗan ba zai bata hannunshi ya taba abinci ba.

Kara karanta wannan

Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa

Sarkin Dirama.
Dirama, Karamin Yaro Ya Murtuke Fuska, Ya Nemi a Ba shi Abinci a Baki Hoto: @Trobeni
Asali: UGC

A bidiyon na barkwanci da Trobeni ta wallafa a shafin TikTok, karamin yaron na zaune a kan kujera ya maida hankali wurin tattaba wayar dake hannunsa.

Yadda aka yi yaron ya ci abincin

Kakar yaron wacce ta kai masa abincin amma ya nuna sam ba shi da sha'awar cin abincin. Ya ci gaba da ture kwanon kuma bai ko daga kai ya kalli menene a ciki ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har sai lokacin da matar da duka kasa da abincin sannan ya amince zai ci, bidiyon yadda abin ya wakana ya haddasa cece-kuce.

Legit.ng Hausa ta gano cewa an wallafa bidiyon a ranar 28 ga watan Disamba, 2022 kuma zuwa yanzun mutane sama da Dubu hudu ne suka kalla.

Bidiyon yadda abun ya faru

Ra'ayoyin jama'a

Rejoice Murnane ta ce:

"Kalle shi ya nuna irin kamar yana da wani muhimmin aiki da zai shirya gabatarwa."

Kara karanta wannan

Yadda Wani Mutum A Abuja Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Birne Gawarsa Saboda Kudi

Nigel ya ce:

"Shin na takura maka ne Oga?"

Satah Kavara ta ce:

"Oga fa baya kaunar ya ci abincin dare"

A wani labarin kuma Kare Ya Kama Uwar Gidansa Na Holewa da Saurayinta a Daki, Ya Ture Shi a Bidiyo

An ga abun mamaki lokacin da wani kare ya tura saurayin uwar gidansa yayin da ya kama su suna rage wa juna zafi a daki.

Lamarin dai ya ba mutane mamaki, wasu na tsammanin kishi ne yayin da wasu ke cewa yana kokarin ba da kariya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel