Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa

Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa

  • Wani magidanci tare da iyalinsa sun nufi kauye domin zuwa hutun sabon shekara amma suka gamu da mushkila
  • Mutumin ya manta da matarsa a tsakiyar daji ya ja motarsa ya tafi sai da yayi tafiya mai nisa ya lura
  • Mutumin ya yi bayanin abinda ya faru lokacin da suka tsaya a hanya yin fitsari yayi tafiyar

Wani mutumi dan shekara 55 ya manta da matarsa da tsakiyar daji yayinda suke hanyar tafiya hutun sabon shekara a kasar waje.

Ma'auratan yan kasar Thailand sun nufi garin Maha Sarakham domin yin shagalin sabon shekara.

Thaii
Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa Hoto: New York Post
Asali: UGC

Mijin mai suna Boontom Chaimoon ne mai tuki sai kawai ya tsaya yin fitsari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda ya sauka, sai matarsa Amnuay Chaimoon, ita ma ta sauka ta zagaya don ta kama ruwa.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon Yadda Wani Yaro Ya Dafi Babbar Waya Ya Koma Kamar Babban Oga Ya Ja Hankali

Mijin ya ce shi ko kadan bai san ta sauka yin fitsari ba a lokacin saboda cikin dare ne misalin karfe 3 suke kuma babu haske.

Yayinda matar ta gama fitsarin ta dawo bakin hanya, sai ta tarar mijin ya ja mota ya tafi.

Bayan jan mota na tsawon kilomita 159.6 zuwa yankin Korat, sai Boontom ya lura matarsa ba ta cikin motar.

Matar kuma ta rasa yadda zata yi cikin daji sai ta cigaba da tafiya har ta ga wani ofishin yan sanda bayan taka sayyadar kilomota 20.

Yadda ya gano bata cikin motan

Sai jami'in dan sandan ya samu kiran wani dan'uwansa wanda ya kira mijin a waya. Sai a lokacin ya duba yaga ashe ya bar matarsa kan titi.

New York Post ta ruwaito cewa Boontom ya yita baiwa matarsa hakuri ta yafe masa, ya ce duk tunaninsa tana bayan mota tana barci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel