Talauci Ne Ta Sako Ni Gaba: Matashi Dan Shekara 21 Da Ya Yi Yunkurin Sace Keke Napep Din Abokinsa A Adamawa
- Yan sanda a jihar Adamawa sun kama wani Muhammed Umar dan shekara 21 kan satar Keke Napep na abokinsa
- Umar ya bada labarin yadda ya karbi Keke Napep din abokinsa da sunan zai kai wata fasinja wani wuri ya dawo cikin minti 30
- Amma bayan karbar Keke Napep din, Umar ya yi niyyar tserewa ne sai dai dubunsa ta cika, ya ce talauci ne yasa ya aikata hakan
Jihar Adamawa - Wani mutum dan shekara 21 a jihar Adamawa, Muhammed Umar, ya fada hannun yan sanda kan zarginsa da tserewa da Keke Napep din abokinsa.
Ya ce talauci ne ya tilasta masa aikata laifin kuma ya nemi a yafe masa, rahoton The Nation.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar The Nation ta rahoto cewa a ranar Juma'a ne Muhammed ya karbi Keke Napep din daga abokinsa, kan cewa zai dawo masa da shi cikin minti 30, amma ya tsere.
Muhammed dan asalin unguwar Shuwari ne a tsohuwar Maiduguri, Jihar Borno amma yana zaune ne a Kasuwan Kuturu a Mubi, Jihar Adamawa.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya bayyana yadda ya shirya tserewa
Ya amsa cewa ya tsere da Keke Napep din bayan abokinsa ya bashi haya a Mubi a makon da ta gabata.
An kama shi ne a Mararaban Mubi da ke kusa.
Ya ce ya rudi abokinsa inda ya fada masa cewa wata mata ta bukaci ya kaita wani wuri a Mubi zai biya N2,000.
Muhammed ya ce ya bawa abokinsa tabbacin cewa zai yi amfani da Keke Napep din na minti 30, idan ya dawo zai bashi N1,500, kuma ya yi amfani da N500 din don siya wa kansa abinci.
Ya amsa cewa a maimakon hakan ya karbi Keke Napep din amma ya bar gari ba da niyyar ya dawo ba.
Mohammed ya roki afuwa, ya ce talauci ta saka shi yunkurin sata
Mohammed ya roki a masa afuwa, yana cewa wannan ne karonsa na farko da ya aikata laifi kuma ya yi ne saboda matsanancin talauci da matsin lamba daga iyayensa.
Yan sanda sun bukaci mai Keke Napep din ya taho ya amshi abinsa
Kakakin yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu idan an kammala bincike.
Ya bukaci wanda ke da Keke Napep din ya taho ya karba a sashin CID na hedkwatar yan sanda da ke Yola tare da shaidan mallaka.
Jami'an tsaro sun dakile harin yan fashin daji a jihar Zamfara
A gefe guda, yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar dakile harin da yan bindiga suka kawo har sau biyu a kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda, Muhammad Shehu ya sanar da hakan yayin holen masu laifi a ranar Asabar a Gusau, rahoton Channels TV.
Asali: Legit.ng