DSS Sun Bar Sabon Gwamna Cikin Hadari, An Dauke Duka Jami'an Tsaron da ke Gadinsa

DSS Sun Bar Sabon Gwamna Cikin Hadari, An Dauke Duka Jami'an Tsaron da ke Gadinsa

  • Hukumar DSS sun dauke jami’ansu da ke tsare da Gwamnan jihar Osun, Mista Ademola Adeleke
  • Ana yada jita-jita cewa Mai girma Adeleke ya ci mutuncin jami’an tsaron ne, sai aka samu matsala
  • Amma wani Hadimin Gwamnan ya ce abin da ya faru sabani ne tsakanin DSS da dakarun ‘yan sanda

Osun - Hukumar DSS masu fararen kaya sun janye Jami’ansu da aka ba aikin tsaron Mai girma gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke.

Daily Trust ta ce a yanzu babu wani jami’in DSS da yake tsare da Gwamna Ademola Adeleke, gidan gwamnatin jihar ko ofishin Gwamna.

Rade-radi na yawo cewa DSS sun janye jami’ansu ne saboda Gwamnan ya ci masu mutunci, Legit.ng Hausa ba ta san gaskiyar batun ba.

A wani jawabi da Mai magana da yawun bakin Gwamnan ya fitar, Olawale Rasheed ya ce sabanin DSS da ‘yan sanda ne ya haddasa matsalar.

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: 'Yan sanda sun kama wasu tsagerun masu garkuwa da mutane

'Dan sabani ne aka samu - Gwamna

Da yake karin haske a yammacin Lahadi, Olawale Rasheed ya nuna cewa babu abin da ya hada Mai girma gwamnan Osun da jami’an tsaron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Cable ta rahoto Rasheed ya ce maganar ta kai hedikwata domin ayi wa jami’an sulhu.

Gwamnan jihar Osun
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

A tsarin mulkin Najeriya, duk abin da ya shafi harkar tsaro ya rataya ne a kan wuyar gwamnatin tarayya, Gwamnan jiha bai da iko a kan DSS.

Zuwa yanzu ba mu ji wata sanarwa daga bakin rundunar ‘yan sanda ko jami’an DSS masu fararen kaya a kan ainihin abin da ya wakana ba.

Ba wannan ne karon farko da aka samu sabani tsakanin dakarun DSS da sojoji, an samu irin haka a fadar shugaban Najeriya a shekarar 2017.

Jawabin Hadimin Gwamna

"Muna so mu yi karin haske cewa ‘yar sabani aka samu tsakanin jami’an hukumar DSS da kuma ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Kai Yaron Gwamnan APC Kotu Bisa Zargin Satar Naira Biliyan 10

An sanar da hedikwatar hukumomin tsaron biyu domin a samu mafita. Ana kokarin shawo kan lamarin.
Muna tabbatarwa al’umma cewa babu wani abin damuwa. Gwamna yana da cikakken tsaro, kuma yana aikinsa.”

- Olawale Rasheed

Rashin adalcin Gwamnati

An ji labari Majalisar Wakilai ta ce gwamnatin tarayya ta fasa gina asibitin FMC a garin Daura, yankin da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito.

Hon. Babangida Ibrahim (APC, Katsina) ya ce bai kamata a sake kai wani asibiti yankin Daura ba, alhali babu babban asibiti a kudancin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel