Babu adalci: Majalisa Ta Bukaci Dauke Asibitin da Ake Shirin Ginawa a Mahaifar Buhari

Babu adalci: Majalisa Ta Bukaci Dauke Asibitin da Ake Shirin Ginawa a Mahaifar Buhari

  • ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun hadu a kan cewa bai dace a gina sabon asibitin FMC a Daura ba
  • Hon. Babangida Ibrahim mai wakiltar Malumfashi/Kafur ya bada wannan shawara, kuma aka karba
  • ‘Dan majalisar ya ce akwai asibitocin tarayya a Katsina da Daura, amma babu ire-irensu a yankinsa

FCT, Abuja – ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun umarci ma’aikatar lafiya ta dauke asibitin FMC da take shirin ginawa a garin Daura da ke jihar Katsina.

Premium Times ta ce majalisar tarayya ta na so a maida wannan asibiti zuwa garin Funtua da ke Katsina, a maimakon a gina ta mahaifar shugaban kasa.

‘Yan majalisa sun cin ma wannan matsaya a ranar Alhamis bayan Hon. Babangida Ibrahim mai wakiltar Malumfashi/Kafur ya bijiro da batun a zaurensu.

Hon. Babangida Ibrahim ya ce akwai dankareren asibitin sojojin sama da aka gina a Daura a shekarar 2019, don haka babu bukatar a sake kai wa yankin FMC.

Kara karanta wannan

Sanatoci na Barazanar Bada Umarnin Cafke Jami’in Gwamnati Kan Bacewar Miliyoyi

‘Dan majalisar ya ce gina wani asibitin tarayya a Daura ba zai taimaki jihar Katsina ba, idan aka yi la’akari da cewa babu wani irin asibitin a shiyyar Funtua.

Majalisa
'Yan Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kukan Hon. Babangida Ibrahim

“A Agustan 2019, gwamnatin tarayya ta kafa asibitin sojojin sama, katafaren gini na zamani da zai magance fita asibitocin kasashen waje da ake yi neman lafiya.
Ba za a taimaki dinbin al’ummar jihar Katsina idan aka bar asibitin FMC a Daura ba duk da asibitin sojoji da ake da shi da kuma kusancin garin da birnin Katsina.
Yankin Funtua na fama da karancin asibitin tarayya, duk da nisansa da irin wadannan cibiyoyin lafiya da ake da su a jihar.” - Hon. Babangida Ibrahim

An ba kwamitoci aiki

Punch ta ce bayan an saurari korafin ‘Dan majalisar na yankin Kudancin Katsina, an amincewa kwamitocin kiwon lafiya da na kula da aikin majalisa su zauna.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Kus-Kus da Wani ‘Dan Takaran 2023, Ya bar Magoya-baya a Duhu

Kwamitocin za su tabbatar da cewa an dauke gina wannan asibiti a Daura, a maida shi Funtua.

Rahoton ya bayyana cewa majalisar tarayya ta bada shawarar a maida babban asibitin garin Daura ya zama asibitin FMC na tarayya domin a ci moriya.

Kwanakin baya aka daga darajar FMC da ke garin Katsina ya zama asibitin koyar da aikin likitoci. Har gobe babu babban asibitoci a kaf yankin Kudancin Jihar.

Ginin asibitin tarayya a Daura zai ci N500m

A baya an ji labari Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ware N500m domin gina gwamnatin asibitin tarayya a garin Daura a kasafin kudin shekarar 2023.

A halin yanzu akwai FMC a garin Katsina, ma'ana babu wata Jihaa Najeriya da take da asibitin har biyu, a daidai lokacin da akwai jihohi 15 da ke neman irinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel