Buhari @80: Na Hannun Daman Tinubu Ya Lissafa Manyan Zarge-zargen Da Aka Yiwa Shugaban Najeriya

Buhari @80: Na Hannun Daman Tinubu Ya Lissafa Manyan Zarge-zargen Da Aka Yiwa Shugaban Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fuskanci zarge-zarge da dama tun bayan da ya hau mulki a 2015
  • Daya daga cikin ikirarin da aka yi shine cewa Buhari ya mutu kuma mutumin da ke Aso Rock Jubrin ne daga Sudan
  • Wani hadimin Bola Tinubu, Joe Ibokwe, ya lissafo wasu daga cikin zarge-zargen da magauta suka yi kan Buhari

Watanni bayan ya hau karagar mulki a 2015, Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke bikin cika shekaru 80 a yau Asabar, 17 ga watan Disamba ya fuskanci zarge-zarge daga magautansa.

Koda dai shugaba Buhari ya hau mulki da niyan kawo chanji, mutane da dana suna ganin ya gaza cika alkawaran da ya dauka yayin yakin neman zabensa bayan ya lashe zabe a 2015.

Muhammadu Buhari
Buhari @80: Na Hannun Daman Tinubu Ya Lissafa Manyan Zarge-zargen Da Aka Yiwa Shugaban Najeriya Hoto: Mbuhari
Asali: Twitter

Joe Ibokwe, wani dan kashenin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, ya lissafa wasu zarge-zargen da aka yiwa shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Kai Yaron Gwamnan APC Kotu Bisa Zargin Satar Naira Biliyan 10

Kalle su a kasa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Sun fadi abubuwa marasa dadi game da PMB

2. Sun kira shi da sunaye iri-iri

3. Sun ce ba shi da lafiya

4. Sun ce Jibrin ne daga Sudan

5. Sun ce bai san komai ba

6. Sun zarge ahi da bangaranci

7. Sun ce bai da takardar shaidar karatu

8. Sun ce bai samu kowani nasara ba a kusan shekaru 8

9. Sun zage tsawon awanni da dama

10. Sun kira shi da bugharia

11. Sun ce mutumin da ke Aso Rock ba PMB bane

12. Sun ce baya iya magana

Da yake rufe wallafarsa, Igbokwe ya ce:

"Ku kalla a yanzu wannan mutumin ya cika shekaru 80 a yau. Kwanan nan ku ka ga an bude gadar Najeriya ta biyu a ranar 15 ga watan Disambar 2022. Za ku ji shi kuma za ku gan shi."

Kara karanta wannan

Bukatu 6 da Muka Gabatarwa Buhari Sa'ilin da Muka Zauna da Shi Inji Aminu Daurawa

Na yi iya bakin kokarina a matsayin shugaban kasa, Muhammadu Buhari

A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya tsawon shekaru bakwai da rabi da suka wuce, ya yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya kawo sauyi a kasar.

Buhari wanda ya ce kasar na da girma da tarin mutane masu yawan gaske, ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin inganta rayuwar matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel