Na Yi Iya Bakin Kokarina a Matsayin Shugaban Kasa, Buhari

Na Yi Iya Bakin Kokarina a Matsayin Shugaban Kasa, Buhari

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi iya bakin iyawarsa a shekaru bakwai da rabi da ya yi a karagar mulki
  • Buhari ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen magance matsalolin da suka addabi matasa domin sune manyan gobe
  • Gidauniyar Abu Dhabi ta ce za ta karrama Shugaba Buhari saboda rawar ganin da ya taka wajen inganta zaman lafiya da tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi iya bakin kokarinsa ga al'ummar Najeriya da ma kasar baki daya.

Buhari ya bayyana hakan ne a Washington yayin da yake maraba da babban sakataren gidauniyar Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa, Fasto Bob Roberts na US wadanda suka ziyarce shi, Daily Trust ta rahoto.

Buhari
Na Yi Iya Bakin Kokarina a Matsayin Shugaban Kasa, Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Buhari ya ce:

"Muna da girma da yawan al'umma, muna fuskantar kalubale da dama amma a bangarori da dama muna kokari. A shekaru bakwai da rabi, na yi iya bakin kokarina."

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Jigo a Najeriya ya fusata kan kin hukunta wadanda suka kashe Deborah

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zamu inganta rayuwar matasa saboda sune manyan gobe, Buhari

Buhari a cikin wata sanarwa daga kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce magance matsalolin da ke addabar matasa shine abun da gwamnati ta baiwa fifiko saboda makomar kasar a nan gaba.

Shugaban kasar wanda ya yi magana game da muhimmancin inganta rayuwar matasa don guje ma masu tsattsauran ra'ayi na addini, ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da tallafawa matasa wadanda sune manyan gobe.

Shugaban kasar ya kuma ce:

"Aikinku na da muhimmanci sosai wajen taimakawa matasa su fahimci juna sannan su rika alfahari da tushensu.
"Wannan babban shiri naku zai taimakawa manyan gobe su shirya sosai sannan su rayu tare cikin zaman lafiya. A bangarenmu, za mu ci gaba da magance matsalolinmu, musamman tunda sun danganci matasa."

Gidauniyar Abu Dhabi za ta karrama Buhari da lambar yabo

Kara karanta wannan

Ta Ya Ka Tara Dukiyarka Idan Gidanku Talakawa Ne? Atiku Ya Aika Sako Ga Tinubu

Bin Bayyah ya bayyana cewa sun zo ne don sanar da shugaban kasar da kuma gayyatarsa zuwa wurin bikin karramawa na gidauniyar Abu Dhabi inda za a bashi lambar yabo saboda nasarorin da ya samu wajen tallata zaman lafiya da tsaro.

Ya kuma bayyana cewa karramawar ta yi daidai da aikin gidauniyar na yaki da tsattsauran ra’ayin addini da kuma tallata zaman lafiya da sulhu tsakanin addinai, rahoton The Cable.

Atiku ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya jihar Filato

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha alwashin cewa idan har ya gaji Shugaba Buhari a 2023, rikicin addini da kabilaci zai zama labari a jihar Filato.

Da yake jawabi a wajen yakin neman zabensa a garin Jos, Atiku ya kuma yi alkawarin farfado da tattalin arzikin jihar Filato idan ya dare kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel