Kotu ta Yankewa Jami’in Hisbah Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya

Kotu ta Yankewa Jami’in Hisbah Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya

  • Alkali Amina Adamu ta babbar kotun tarayya dake Kano ta yankewa tsohon jami’in Hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Laraba
  • Alkali ta kama Dayyabu da laifin halaka wata bazawara mai suna Hauwa da yaso aure amma ta ki aurensa bisa umarnin iyayenta
  • Dayyabu ya same ta har gida inda yace mata yazo su yi sallama amma ya dinga soka mata wuka a sassan jikinta har ta rasa ranta

Kano - Wata babbar kotu dake zama a jihar Kano mai lamba 9 ta yankewa wani tsohon jami’in Hisbah mai suna Dayyabu Muhammad hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Dayyabu
Kotu ta Yankewa Jami’in Hisbah Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya. Hoto daga Aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Alkali Amina Adamu ce ta yanke hukuncin kan tsohon jami’in Hisban da ya halaka wata bazawara mai suna Hauwa Ibrahim.

Alkali tace laifin ya ci karo da sashi na 221 na kundin Penal Code.

Kara karanta wannan

"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Aminiya ta rahoto cewa, Dayyabu yayi aiki a Hisbah kuma almajiri ne a gidansu Hauwa, ya nuna bukatar aurenta har suka zurfafa a soyayya.

A karshe Dayyabu ya fara zancen aure amma iyayen Hauwa suka dire gefe suka ce basu aminta da tarbiyyyarsa ba kuma ba zasu bashi auren diyarsu ba.

Sai kuma daga bisani Hauwa ta nuna bata da ra’ayin aurensa ita ma.

Wannan lamarin ya fusata Dayyabu wanda ya je gidansu Hauwa a shekarar 2011 kan cewa ya zo su yi sallama.

Marigayiyar tana kwance a cikin daki yayin da yaje.

A nan ya dauko wuka ya dinga soka mata a jikinta, lamarin da yayi sanadin mutuwarta har lahira.

Alkali Amina Adamu yayin yanke hukuncin tace ta samu gamsassun hujjoji daga masu gabatar da kara wanda ya tabbatar da cewa an kama shi da laifin da ake tuhumarsa, hakan yasa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

Kotu ta yankewa budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya

A wani labari na daban, wata kotu dake zama a jihar Kano ta yankewa wata budurwa mai suna Aisha hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun ta kama Aisha da laifin kisan makwabciyarta mai suna Bahijja wacce fada ya hada su.

An gano cewa Aisha ta kira Bahijja da karuwa amma Bahijja ta kwashi kawaye inda suka je suka lakadawa Aisha duka wanda a nan ne ta halaka Bahijja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel