Kano: Kotu Ta Yankewa Budurwa Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya

Kano: Kotu Ta Yankewa Budurwa Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya

  • Wata babbar kotun tarayya mai zama a Miller Road dake birnin Kano, ta yankewa wata budurwa hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Alkali Amina ta yankewa Aisha hukunci ne bayan ta kama ta da laifin halaka makwabciyarta mai suna Bahijja bayan fada ya hada su
  • Kamar yadda lauyanta yace, mamaciyar da kanta ta bi wacce aka yankewa hukunci wurin aikinta tare da lakada mata duka, lamarin da yasa aika-aikar ta faru

Kano - Babbar kotun tarayya dake zama a Miller Road dake jihar Kano ta yankewa wata budurwa hukuncin kisa a ranar Laraba bayan halaka makwabciyar ta, Aminiya Daily Trust ta rahoto.

Budurwa a kotu
Kano: Kotu Ta Yankewa Budurwa Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Alkali Amina Adamu dake kotun ta yankewa budurwa Aisha Kabir hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan tsawon shekara daya da aka yi ana tafka shari’ar.

Kara karanta wannan

Idan da Rai: Bayan Shiga Jami'a a 1951, Tsohuwa mai Shekaru 90 ta Kammala Digirinta

Aisha ta gurfana gaban kuliya ne bayan an zargeta da burmawa makwabciyarta Bahijja wuka a wuyanta bayan sabani ya hada su.

An fara rigimar ne bayan Aisha ta kira Bahijja da karuwa kuma hakan ya haddasa gagarumar rigima a tsakaninsu wanda ya kai ga Aisha ta soka mata wuka kuma ta mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Laraba yayin zaman kotun, Alkalin tace ta kama wacce ake zargin da laifin kuma ta yi hukuncin halaka ta ta hanyar rataya.

A yayin tsokaci kan hukuncin, Barista Auwal Abubakar Ringim, lauyan dake kare Aisha, yace ba zasu ce komai a kan hukuncin ba sai sun nazarci shari’ar.

“Lamarin da ya auku shi ne, an samu hatsaniya tsakanin wacce ta rasu da wacce aka yankewa hukunci. Daga bisani mamaciyar tare da kawayenta suka garzaya wurin aikin Aisha suka lakada mata duka. A nan ne lamarin ya faru.”

Kara karanta wannan

Budurwa ta Kwace Motar da ba Saurayinta bayan Shekatu 2 da Suka Rabu, Kazantar da ta Gani Ciki ta Tada Hankali

- Cewar Barista Ringim.

’Yan uwan Bahijja sun yi martani

A bangarensu, Danlami Abbas, ‘dan uwan Bahijja ya bayyana farin cikinsa kan hukuncin da aka yanke inda yace an yi adalci.

Barista Lamido Abba Sorondiki, wanda lauyan gwamnati ya sanar da gamsuwa da hukuncin da kotu ta yanke.

Yace sun jiran daukaka karar wadanda aka yi kara.

Dan China ya halaka budurwarsa a Kano

A wani labari na daban, wani ‘dan China mazaunin birnin Kano ya sokawa budurwarsa wuka.

Lamarin ya faru a Janbulo dake cikin kwaryar birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel