Budurwa Ta Shiga Tasku Bayan Mahaifiyarta Ta Gano Hirar Da Suka Yi Da Saurayinta a Waya, Bidiyon Ya Yadu

Budurwa Ta Shiga Tasku Bayan Mahaifiyarta Ta Gano Hirar Da Suka Yi Da Saurayinta a Waya, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiya ta cika da tsoro bayan mahaifiyarta ta karbi wayarta sannan ta fara duba hirarta da mutane
  • A bidiyon da Sylva ta wallafa a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, mahaifiyarta na ta duba hirarta kamar tana neman wani abu
  • Sa'o'i 24 bayan wallafa bidiyon, sauran masu amfani da TikTok sun bayyana yanayi makamancin wannan da suka taba riskar kansu a ciki

Wata matashiya a TikTok ta wallafa bidiyon lokacin da mahaifiyarta ta binciki wayar kanwarta.

Sylvia ce ta wallafa bidiyon a ranar Talata, 12 ga watan Disamba sannan ya nuna yadda mahaifiyarta ta binciki hirar yarinyar.

Yan mata da waya
Budurwa Ta Shiga Tasku Bayan Mahaifiyarta Ta Gano Hirar Da Suka Yi Da Saurayinta a Waya, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Tommaso79/Getty Images, TikTok/@only_1_sylvia
Asali: UGC

A bidiyon mai tsawon sakan 14, an gano mahaifiyar na bibiyar hirar kamar mai neman wani abu da bata yarda da shi ba.

Yayin da mahaifiyar ke duba wayar, matashiyar ta zauna shiru kamar wacce ke cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Budurwa ta bi Saurayi a Wurin Biki ta Tashe shi, Zai Aureta Bayan Shekaru Uku a Bidiyo

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hatta Sylvia wacce ta wallafa bidiyon ta ce kanwar tata zata sha mazga, amma ba a san ya lamarin ya kaya ba.

Hakazalika, ba a sani ba ko uwar ta gano wani abu da bata so a wayar diyar tata.

Sai dai mutanen da sun yi martani kan bidiyon sannan sun bayyana cewa irin haka ta taba faruwa da su.

Kalli bidiyon a kasa:

Martani daga masu amfani da TikTok

@dammy ta ce:

"Irin haka ya taba faruwa da ni ahhh ban ji ta da dadi ba.
"Kawai tana ta kuka sannan mahaifina na ta bani mari mai lafiya a duk sanda hawaye ya dira daga idonta."

@Biggeat Goldie ta ce:

"Iyayenmu basu san sirri ba."

@Tifeh ta yi martani:

"Wannan ne dalilin da yasa ya kamata ka dunga ahare hirarka da mutane a duk sanda kuka gama hura. Musamman idan ba da kudinka ka siya wayanta."

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Gano Mijinta Ya Yi Amarya a Ɓoye Har Sun Haihu, Ta Je Gidan An Buga Dirama a Bidiyo

@underson ya ce:

"Yadda yarinyar ta zauna. Baaaba ina iya jin bugun zuciyarta."

Magidanci ya gano diyarsa ba tasa bace bayan yi mata gwajin DNA

Wani magidanci ya shiga damuwa bayan ya gano diyarsa da yake tsananin so ba shine ainahin ubanta da taimakon gwajin kwayar halitta.

Mutumin ya dauki yarinyar cikin sirri sannan ya kaita aka yi mata gwaji saboda yana kokwanton kasancewarsa diyarsa kuma sakamako ya nuna ba tasa din bace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel