‘Yar Najeriya Tayi Amfani da Ledar Fiyo Wota Ta Dinka Hadaddiyar Riga

‘Yar Najeriya Tayi Amfani da Ledar Fiyo Wota Ta Dinka Hadaddiyar Riga

  • Adejoke Lasisi, wata mata 'yar Najeriya mai matukar fasaha wacce tela ce ta maida ledojin fiyo wota da aka yi amfani aka dinka hadaddiyar riga
  • Matar, wacce ke aiki a sashin kula da muhalli, ta kyace a cikin shiga mai daukar hankali a wasu hotuna da aka wallafa a yanar gizo
  • Wasu 'yan soshiyal mediya da suka yi tsokaci bayan yin arba da hotunan a yanar gizo sun tsunduma kogin mamaki da irin matukar kayatarwan da tayi

'Yan Afirka na da matsalar gurbataccen mahalli duba da yadda ake zubda abubuwa ba tare da nazarin kan illarsa ga rayuwar bil'adama ba.

Rigar fiyo wota
‘Yar Najeriya Tayi Amfani da Ledar Fiyo Wota Ta Dinka Hadaddiyar Riga. Hoto daga @jack
Asali: UGC

Sai dai wasu masu fasahar kera abubuwa suna taimakawa wajen maida su abubuwan amfani don shawo kan matsalar da ake fuskanta.

Adejoke Lasisi, wata mata 'yar Najeriya ta hada riguna daga ledar fiyo wata da aka zubar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ke Sharholiya Cikin Kaji Ya Dauki Hankali, Ta Zama Kamar Shugabarsu

Matar dake zaune a kasar Ghana wacce ke da kamfanin Mckingtorch Makafui Awuku, ta samar da kaya daga ledar fiya wata da aka zubar ta hanyar amfani da wani solin saka don dawo da su abun ban sha'awa da daukar hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wallafar da @jack yayi a dandalin Twitter ya jawo cecekuce inda ya ce:

"Abokiyar aikina kuma kawata Adejoke Lasisi wacce ke aiki a sashin kula da muhalli a Najeriya tana hada yadin kaya daga ledar fiyo wata da aka zubar, sannan tana amfani da wani salon saka kente don dawo dasu abun sha'awa da daukar hankali.
Ku kalli irin rigar da take sanye da ita. Ta samo yadin ne daga sarrafaffen ledojin fiyo wata,"

- Inda ya wallafa da hotunan.

An dauki hoton Lasisi ne a wani kamfani masoyinta inda ta kyace cikin hadaddiyar riga. Ta cikasa wankan ta ne da jakar da ta shiga da kayan.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon yadda aka kirkiri injin kyankyasar jariran dan Adam

Jama’a sun yi martani

Yayin da masu tsokaci ke ta yabawa da wankan Lasisi, wasu hankalinsu gaba daya rigar ta tafi dashi.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin.

Trudy ta ce:

"Kai, kodai wasa ka ke! Wannan ya matukar kayatarwa."

Nun Ana tayi martani:

"Kai, gaskiya ina son koyan yanda ake yi."

Aask Selasi Awerwra tayi tsokaci:

"Gaskiya ya matukar haduwa! Kaiiiii."

Josephine Ndanemah ta ce:

"Wannan ya kayatar matuka."

Dziany Stella ta ce:

"Kaiiii, idan da ace muna da taren masu hazaka haka da mun ji dadi."

Maame Abena Ruth tayi martani:

"Amma a zahiri, mutane nada basira, kuma suna tunani faaa, dubeni, ina nan ina cin banku."

Roos Als ta ce:

"Hakan ya matukar burge ni; abu ne mai kyau!"

Catherine Michelle tayi tsokaci:

"Gaskiya yayi kyau kuma fasahar tayi kyau."

Kara karanta wannan

2023: Na Gode Allah da Tinubu Bai Zabe Ni a Matsayin Abokin Takara Ba, Tsohon shugaban Majalisa

Adejoke Lasisi ta ce:

"Ina matukar godiya da kuka wallafa kamfanin 'dan uwana Mckingtorch Makafui Awuku ina matukar godiya."

Esi Ladi ta ce:

"Kaiii! Abun sha'awa!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel