Aljannar Duniya: Matashin Miloniya Ya Kammala Gidansa, Ya Kawata Shi Tamkar ‘Fadar Sarki’

Aljannar Duniya: Matashin Miloniya Ya Kammala Gidansa, Ya Kawata Shi Tamkar ‘Fadar Sarki’

  • Wani matashi dan Najeriya ya garzaya soshiyal midiya domin nuna gidan da ya ginawa kansa ba tare da ya yi tunanin fara siyan mota ba
  • Da yake wallafa bidiyon cikin gidan da ya kawata da kayan alatu, mutumin ya bayyana cewa ya ji dadin hanyar da ya bi wajen kashe kudinsa
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani ga bidiyonsa sun bayyana cewa sun ji dadin yadda ya fi bayar da muhimmanci wajen mallakar gida

Wani matashi dan Najeriya mai suna @bansi342 wanda duniya bata san irin sana’arsa ba yake yi ba ya baje kolin katafaren gidan da ya ginawa kansa.

Da yake wallafa bidiyon gidan a yanar gizo, matashin ya girmama batun mallakan gida fiye da kashe miliyoyin kudi kan motoci. Ya yi bidiyon cikin harabar gidan nasa wanda ke babur fake a cikinsa.

Kara karanta wannan

Maa Ta Nadi Bidiyon Mijinta Yana Shan Wankin Kayanta, An Yi Cece-kuce

Matshi da gida
Aljannar duniya: Matashin miloniya ya kammala gidansa, ya kawata shi tamkar ‘fadar sarki’ Hoto: TikTok/@bansi342
Asali: UGC

Cikin gidan ya hadu iya haduwa

A wani bidiyon kuma, matashin ya bayyan cewa ya gamsu da yadda yake kashe kudadensa. Ya kawata gidan ta yadda kana ganinsa z aka san kudi ya yi kuka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan Najeriya da dama da basu damu da sanin daga ina tushen arzikinsa yake ba sun yi tururuwan zuwa sashin sharhi domin jinjina masa tare da taya shi murna.

Ga bidiyon cikin gidan a kasa:

Jama'a sun yi martani

commentator

“Na tayaka murna amma biyan haya ba talauci bane idan har mutum yana da kudin. A bar mu da motarmu da gidan hayanmu.”

John Chukwuebuka y ace:

“Ka rike matsayinka babu wanda ke gasa da kai.”

Wealthcome ya ce:

“Na tayaka murna dan uwa..Na so wannan kuma ina fatan samun irinsa nima.”

baby face ta ce:

Kara karanta wannan

Dala 500k/N220m: Tulin miliyoyin da dan Najeriya ya kai banki zai ajiye ya girgiza jama'a

"Chaiii. Kalli gida ina tayaka murna. Nima ina rokon samun irin haka don nayi murnar nawa nan kusa.”

Mr P ya ce:

“Kai namiji ne dan uwa ina maka fatan samun karin kadara, wa ya ce abun da sauki a bari ya je ya tambayi farashin siminti, mota ba nasara bane amma mutane da dama basu fahimci haka ba.”

Matashi ya kerawa kansa gida na gani na fada

A wani labarin, wani matashi ya cika da farin ciki yayin da ya gwangwaje kansa da wani hadadden gida na gani na fada.

Mabiya shafukan soshiyal midiya da dama sun taya shi farin ciki yayin da wasu ke jin ina ma ace sune a matsayinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel