"Ba Mu Iya Barci da Idanu 2," Dan Majalisar Ya Kai Korafin Halin da Suke Ciki a Mazabarsa

"Ba Mu Iya Barci da Idanu 2," Dan Majalisar Ya Kai Korafin Halin da Suke Ciki a Mazabarsa

  • Wani ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya ce yawaitar satar mutane ya sa mazauna mazaɓarsa suka rasa kwanciyar hankali
  • Solomon Yakubu Akwashiki ya ce an sace mutum biyu a Agyaragu Lafia, inda masu garkuwar ke neman kuɗin fansa
  • Majalisar dokokin jihar ta buƙaci Gwamna Abdullahi Sule ya umarci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lafia, jihar Nasarawa – Ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar mazaɓar Lafia ta Tsakiya, Hon. Solomon Yakubu Akwashiki, ya ce yawaitar satar mutane a yankinsa ya sa mazauna wurin kasa kwanciya su yi barci da ido biyu.

Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne a zaman majalisar ranar Talata, lokacin da ya gabatar da batun a matsayin wani lamari da ya shafi al’umma, inda ya buƙaci jami’an tsaro da gwamnatin jihar su ƙara himma wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun farmaki dan majalisar tarayya na APC a Kano da duwatsu

Nasarawa.
Harabar Majalisar dokokin jihar Nasarawa da ke birnin Lafia Hoto: Danladi Jatau
Source: Facebook

A cewarsa, an sace mutum biyu a Agyaragu Lafia a ranar Litinin, yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu mutane a Agunji Lafia kwanakin baya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya ce har zuwa lokacin da yake magana, mutanen biyu da aka sace a Agyaragu suna hannun masu garkuwa da mutane, waɗanda ke neman a biya su kuɗin fansa.

An nemi ɗaukar matakin gaggawa

Da yake magana a zauren majalisar, Akwashiki ya ce:

“Mai girma Shugaban Majalisa da abokan aikina, na tashi ne domin gabatar da batun yawaitar satar mutane a mazaɓata. Jiya, an sace mutum biyu a Agyaragu Lafia. Kwanaki kaɗan da suka gabata kuma, an yi garkuwa da wasu mutane a Agunji Lafia.
“Yayin da nake magana a yanzu, mutanen biyu da aka sace jiya suna hannun masu garkuwa da mutane, kuma suna neman kuɗin fansa.
“Ya kamata jami’an tsaro da gwamnatin jihar Nasarawa su tashi tsaye domin shawo kan yawaitar satar mutane da sauran matsalolin tsaro a mazaɓata."

Kara karanta wannan

Siyasa na ɗaukar zafi, ƴan daba sun farmaki ɗan takarar majalisa, an rasa rai

Majalisa ta aika sako ga Gwamna Sule

Da yake mayar da martani kan sabon ƙaruwa da aka samu na satar mutane a fadin Nasarawa, Shugaban Majalisar Dokokin, Danladi Jatau, ya ce babban birnin jihar da wasu yankuna na fuskantar yawaitar garkuwa da mutane.

Jatau ya yaba wa wanda ya gabatar da ƙudurin da sauran ’yan majalisar bisa gudummawar da suka bayar kan matsalar.

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule yana jawabi a wurin taro Hoto: Abdullahi A. Sule
Source: Twitter

Ya bayyana cewa ƙudurin majalisar shi ne a buƙaci Gwamna Abdullahi Sule ya umarci dukkan hukumomin tsaro, ciki har da rundunar ’yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC), su ƙara sanya ido domin rage yawaitar satar mutane.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar sarakunan gargajiya, dagatai da masu unguwanni da jami’an tsaro na sa-kai wajen gano baƙin mutanen da suka shigo al’ummominsu.

Shugaban majalisar ya umarci magatakardar majalisar da ya aika da ƙudurin ga Gwamna Sule domin ɗaukar matakin da ya dace.

An kama masu safarar makamai a Nasarawa

Kara karanta wannan

'Yan daba sun farmaki ayarin ɗan takarar jam'iyyar su Kwankwaso, an kashe mutum 1

Kun ji cewa hukumar DSS ta kama wata mata mai shekara 23 da wasu mutum huɗu da ake zargi da safarar makamai, a wasu samame daban-daban da ta gudanar a Jihar Nasarawa.

A yayin samamen, jami'an hukumar sun kwato harsasai sama da 2,000, ciki har da na bindigogi kala daban-daban daga wadanda ake zargi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262