Babu Wanda Ya Tuhumi Wadanda Suka Kashe Deborah, in Ji Tsohon Shugaban NERC

Babu Wanda Ya Tuhumi Wadanda Suka Kashe Deborah, in Ji Tsohon Shugaban NERC

  • Jigon Najeriya ya bayyana damuwa game da rashin hukunta wadanda suka hallaka Deborah Samuel a jihar Sokoto
  • An hallaka wata daliba tare da kone gawarta bayan fitowar wani sakon murya da aka ji tana batanci ga Annabi Muhammadu SAW
  • Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana hukuncin da aka yiwa wadanda aka kama bisa zargin aikata wannan kisan ba

Tsohon shugaban hukumar kula da wutar lantarki, Sam Amadi ya bayyana damuwa game da rashin daukar matakin adalci kan kisan da aka yiwa Deborah Samuel, dalibar kwalejin da aka kone ta bisa zargin zagin Annabi (SAW).

Dalibai sun hallaka tare da kone gawar Deborah, dalibar aji biyu a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto a watan Mayun 2022 bayan fitowar wani sakon murya da aka ji tana dura ashariya ga fiyayyen halitta.

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

A shafinsa na Instagram a ranar Litinin, Amadi ya bayyana kukansa da shiga damuwa bisa gaza hukunta wadanda suka kashe dalibar, Punch ta ruwaito.

Har yanzu ba a hukunta makasan Deborah ba, inji Sam Amadi
Babu Wanda Ya Tuhumi Wadanda Suka Kashe Deborah, in Ji Tsohon Shugaban NERC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, babu wanda aka hukunta saboda Najeriya na ci gaba da zama kasa mai yiwa ‘yan tsaurin addini sako-sako.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya rubuta cewa:

“Babu wanda aka kama aka gurfanar saboda kisan Deborah. Babu wanda zai yi hakan. Wannan ya faru ne saboda ana tafiyar da Najeriya ne a matsayin kasa mai bin tsarin tsaurin addini.
“Hanyar ci gaban Najeriya ta ta’allaka ne da wargaza tubalin addini na kafuwar kasa mai suna Najeriya. Saboda haka, Najeriya na ci gaba da kasancewa kasa mai aminta da tsaurin addini.”

Laifin IGP da gwamna Tambuwal ne

Amadi, wanda dan gwagwarmaya ne ya zargi sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba da gwamnatin jihar Sokoto da kin tabuka komai wajen ganin an gurfanar da wadanda suka kashe Deborah.

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Amadi ya kara da cewa:

“IGP ko gwamna Tambuwal basu yi komai wajen kamewa da gurfanar da wadanda suka kashe Deborah ba sabo idan muka yi haka, za mu fusata wasu mahaukata ‘yan tsaurin addini, wadanda ka iya yin hauka. Sakamakon irin wannan tashin hankali zai iya shafar siyasa.”

A cewar Amadi, addini na daya daga cikin abubuwan da ke mai da Najeriya baya a hakin da ake ciki a yanzu.

Rubutun Amadi a shafin Instagram na zuwa ne bayan da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya bayyana dalilin da yasa ya goge rubutun yin Allah wadai da ya yi da kashe Deborah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel