An zargi jami’in NSCDC da damfarar masu neman aiki Har N12.2m

An zargi jami’in NSCDC da damfarar masu neman aiki Har N12.2m

  • Zargin cin hanci ko rashawa wajen neman aiki a nigeria ya zama ruwan dare, da yawa daga yan kasar na zargin sai kana da farcen susa zaka samu aiki
  • Wanda Hukumar ICPC ta gabatar a gaban kuliya kan damfarar mutane sufeto ne na rundunar NSCDC din da suke kare dukiyoyin al'umma, amma yana cikin wanda suke zambatar mutane
  • Neman aiki ya zama wata masana'anta mai zaman kanta a Nigeria, kamar yadda hukumar kiddiga ta NBC, ta sanar da kaso 60 na matasan kasar basa aiki

Abuja: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da wani Sufeto na hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC, Solomon Ogodo a gaban kotu bisa zarginsa da zamba cikin aminici.

Mai magana da yawun hukumar, Azuka Ogugua, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis din nan, kamar yadda jaridar The Punch ta hakkaito

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Tuhumar kwafin karar mai lamba CR/503/2022 wadda taje gaban mai shari’a MS Idris na babbar kotun birnin tarayya da ke zamanta a Jabi, Abuja, ta zargi wanda ake tuhuma da damfarar wasu masu neman aikin, har naira miliyan 12,200,000.

Mai Ake Zarginsa Da Aikatawa

Akwai akalla tuhume-tuhume biyar da ake masa, kuma hukumar ta shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhumar a lokuta daban-daban ya danfari mutane da dama makudan kudade da sunan nema musu aiki a hukumomin gwamnati.

Duk datulin zargin da hukumar ta gabatar a gaban mai shari'a, wanda ake tuhuma, yace bashi da laifi, kuma bai aikata abinda ake zarginsa da aikatawa ba, inda yace sharri ne kawai wasu suke masa. Rahaton The Punch

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NSCDC
An zargi jami’in NSCDC da damfarar masu neman aiki Har N12.2m Hoto: The Punch
Asali: UGC

Lauyan da ke kare Mista Osita Eze, ya mika bukatar neman belin wanda yake karewa, wanda lauyan ICPC, Mista Mashkur Salisu bai soki lamirin lauyan wanda ake karar ba kan ko a ki badashi ko kuma a badashi.

Kara karanta wannan

An Samu Karin Talauci Duk Da Tallafin N3.5tn DaGwamnatin Tarayya Ta Bayar

An dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 16 ga watan Junairu shekarar 2023, domin sauraren karar, yayin da alkalin kotun ya amince wanda ake tuhuma da bayar da belinsa a kan kudi N5m tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel