Cibiyar "CHATHAM" Ta Landan Ta Gayyaci Peter Obi Don Tattaunawar Kan Manufofinsa

Cibiyar "CHATHAM" Ta Landan Ta Gayyaci Peter Obi Don Tattaunawar Kan Manufofinsa

  • A farkon wannan satin cibiyar ta gayyaci Bola Ahmed Tinubu dan ya bayyana irin manufofin da yake dasu ga Nigeria
  • Cibiyar dai ta kware wajen kula da harkokin siyasa, musamman a 'kasashen Afrika
  • Ana sa ran 'dan takarar jam'iyyar LP ma zai halacci tattaunawar dan bayyana manufofinsa da kudirrikansa

Landan: Cibiyar kula da siyasa da ha'da muhawara ta kasar Birtaniya wadda ke da ofis a Landan ta gayyaci 'dan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi kan ya yaje domin bayyana manufofinsa da kum amsa wasu tambayoyi

Sanarwar gayyatar dai ta fito ne ta shafin cibiyar a 'kafar twitter inda take nuna rana, lokaci da kuma wajen da za'a tattauna da Obin.

Peter Obi dai na takarar ne da Datti Babba Ahmed a jam'iyyar Labour Party jam'iyyar da ake ganin bata da rinjaye a tsakanin yan kasa. Rahotan Chnnels Tv

Kara karanta wannan

Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne

Wasu na yiwa jam'iyyar kallon jam'iyya ce ta yan yanki daya kawai, ba wai duk fa'din Nigeria ba.

Peter Obi
Cibiyar Chatham Ta Landan Ta Gayyaci Peter Obi Don Tattaunawar Kan Manufofinsa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

TInubu Bai Halarci Muhawara da ‘Yan Takara Ba, Da Gidan Talabijin Na Arise Ya Shirya

'Dan takarar shugaban ‘kasa a jam’iyyyar All progressive Party (APC), Bola Ahmed Tinubu, bai halarci muhawara da ‘yan uwansa ‘yan takarar shugaban kasa ba da gidan talabijin na Arise ya shirya.

Kwamitin ya’kin neman zaben Tinubun yace ba wani tsarin mulki da kasa tasa wanda ya wajabtawa ‘dan takarar tasu zuwa wata muhawara, da wani, ko wata gidan jarida suka shirya.

Kwamittin yace gidan talabijin na Arise bai musu adalci ba, ta hanyar da zai fadawa duniya cewa basu halaci muhawara ba, alhalin suna da taro ne ranar.

Kara karanta wannan

Siyasa Ba Hauka ba ce, Peter Obi ya Fadi Dalilinsa na Mutunta ‘Dan takaran PDP, Atiku

Idan mai karatu zai iya tunawa dai ko shugaba Muhammadu Buhari sai da ya halarci irin wanna taron gabannin zabensa da kuma lokacin da'aka rantsar dashi a matsayin shugaban kasar Nigeria.

Bukatar 'yan Nigeria a yanzu shine samun jajiirtattcen shugaban da zai maida hankali kan abubuwan da suka damesu, musamman a fannin lafiya, tsaro ilimi, fasahar sadarwa da wasu abubuwa makamantansu.

Za'ai babban za'ben Nigeria a watan Fabairu inda za'a fara dana shugaban kasa da 'yan majalissar dokoki sai kuma na gwamna da 'yan majalissar jiha a watan Maris na shekarar 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel