Ba Dole Ne Fa Tinubu Ya Rika Halartar Muhawara Ba, Jam'iyya APC

Ba Dole Ne Fa Tinubu Ya Rika Halartar Muhawara Ba, Jam'iyya APC

  • Dan Takarar Jam'iyyar APC a Shugabancin Kasa Bai Halarci Muhawara Da Gidan Talabijin Din Arise Ta Shirya A Farkon Watan Nuwanban Da Ya Shude
  • Jam'iyyar APC Tace Ba Dole Ne Tinubu Ya Ringa Halartar Muhawar Yan Takara ba, Musamman Ma In Yana Da Abinyi
  • Mai Magana da yawun Dan Takarar Jam'iyyar PDP Sen. Dino Malaye Yace Tinubu Bazai Iya Muhara Da Atiku Ba

Abuja: A cikin wata sanarwa da Kwamitin yakin neman zaben Tinubu ta fitar ta ce kundin tsarin mulkin nigeria bai wajabtawa dan takararta halartan muhawarar da wata kungiya ta shirya ba, kamar yadda Kafar Premium Times ta rawaito

Tinubu
An Nemi Da A Kakabawa Gidan Talabijin Na Arise Takunkumi Inji Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A wata sanarwa da Arise TV ta fitar kwanan nan ta bukaci dukkan ‘yan takarar da su mutunta kundin tsarin mulkin kasar kuma su halarci muhawarar da ta shirya.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Karfafawa Kiristocin Nigeria Gwuiwa, Yace Kar Su Ji Tsoron Zaben 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A baya dai Tinubu ya ki amsa gayyatar tun farko, har ma ya sha alwashin ba zai halarci wasu muhawarar ba.

"Ina tsammanin duk 'yan takarar da ke neman zabe kuma su kafa gwamnati a karkashin wannan tsarin mulki, ya kamata su mutunta doka, tare da halartar tarurrukan muhawara da kafafen yada labarai suke shiryawa" Arise TV. in ji sanarwar.

Tinubu ya ki amsa gayyatar Muhawarar a karon farko wanda aka shirya kan kan tsaro da tattalin arziki a ranar 6 ga watan Nuwamba. Ya ce muhawarar ta ci karo da jadawalin yakin neman zabensa.

An maye gurbinsa da Kola Abiola, dan takarar jam’iyyar Peoples Redemption Party. sai kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu wakilcin abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyun Siyasa sun Magantu Kan Zabin Kungiyar Su Dogara Na Dan Takarar Shugaban Kasa

Ba za ku iya yi mana baki ba

APC ta zargi gidan talabijin din da nuna son kai ga Tinubu kuma ta sha alwashin ba za ta halarci duk wata muhawara da Arise TV ta shirya ba.

“Mun lura da cewa Arise News ta kuma shirya yakin neman zaben ‘yan takarar shugaban kasa da sunan muhawarar ta hanyar amfani da sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Duk da cewa ya dace kafafen yada labarai suna da aikin da kundin tsarin mulki ya ba su karara na su riga sanar da aiyukan mukaman gwamnati ga ‘yan kasa da kuma rawar da suke takawa a matsayinsu na masu sa ido ga al’umma, amma babu wani bangare na kundin tsarin mulki da sashe na 22 da ya ce dan takarar shugaban kasa ya halarci taron Arise News Town Hall ba ko duk wani taron da aka shirya a kafafen yada labarai kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana

Mai Ya Hana Tinubu Zuwa Muhawarar?

Kuma abinda ya hana Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zuwa wannan muhawarar shine; yana da nasa jadawalin ayyukan yakin neman zabe da sauran al’amura a ciki da wajen Najeriya.

Daya daga cikin irin wannan taron shi ne taron da ya shirya yi a ranar Litinin, 5 ga Disamba, 2022 a Chatham House da ke Landan inda zai yi magana kan Tsaro, Tattalin Arziki da Manufofin alaka da kasashen waje, in ji kwamitin.

“Muna amfani da wannan damar wajen gargadin masu magana da yawunmu da magoya bayanmu da su kaucewa wannan tasha bisa rashin da’a da nuna son kai ga dan takararmu da jam’iyyarmu,” inji ta.

A watan Nuwamba,Kwamitin yakin neman zaben Tinubu ya rubuta koke ga hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBC) inda ya bukaci a kakaba wa Arise TV da sauran kafafen yada labarai takunkumi.

Kara karanta wannan

Badakalar N260m: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau shekaru 35 A Gidan Dan kande

Asali: Legit.ng

Online view pixel