Gidan Biki Ya Kacame Yayin da Dambe Ya Kaure Tsakanin Ango Da Wani Da Ya Lika Masa Kudi, Bidiyon Ya Yadu

Gidan Biki Ya Kacame Yayin da Dambe Ya Kaure Tsakanin Ango Da Wani Da Ya Lika Masa Kudi, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani dan gajeren bidiyo ya nuno lokacin da wani ango wanda yayi kicin-kicin da fuska ya ki yarda wani ya lika masa kudi
  • Angon ya kai hannu a lokacin da dan taya murnar ya dage sai ya lika masa wannan kudi
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun kula cewa mutumin ya tofa yawu kan kudin kafin ya lika shi

Wani bidiyo da shafin @somalisnaps ya wallafa a intanet ya nuno yadda wani shagalin biki ya kacame da koma fada.

Yayin da amarya da angon ke rawa a filin biki, sai ga wani dan gayya da ke zaune a gefe ya tashi sannan ya likawa angon kudi.

Shagalin biki
Biki Ya Kacame Yayin da Dambe Ya Kaure Tsakanin Ango Da Wani Da Ya Lika Masa Kudi, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@somalisnaps
Asali: UGC

Ango da dan taya murna sun ba hammata iska

Angon wanda bai ji dadin yadda mutumin ya manna masa kudin a goshinsa ba ya cire shi. Bidiyon ya nuno yadda mutumin ya tofa yawu a kudin kafin ya lika shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami'ai Tafka Sata a Gwamnati

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganin cewa angon ya cire kudin, sai mutumin ya koma dauki kudinsa tare da kokarin sake mannawa angon kuma nan take sai fada ya kaure a tsakaninsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani ga bidiyon

Bidiyon ya haifar da martani daga wadanda suka kalle shi. Yayin da wasu suka ce mutumin ya tofa yawu a kudin tukuna, wasu sun ce hakan al'ada ce.

ibrahym_hassan ya ce:

"Aiki daya mai daukar kamara ke da shi kuma ya gaza."

tom_mogusu ya ce:

"Wannan shine shugaban kauyen yana masa auren dole."

nkunimwellington ya ce:

"Ya tofa yawu kan kudin kafin ya lika masa a goshi, ku kula."

ehiglamoure ya ce:

"Ku duka da kuke martani baku ga abun da ya faru ba bani da tabbacin a Najeriya haka ya faru da sun lallasa mutumin da gani kawunsa ne."

Kara karanta wannan

Dole Ta Yi Masa? Ango Ya Yi Jugum Yana Kallon Amaryarsa Yayin da Take Girgijewa Ita Kadai A Bidiyo

Ango ya yi kicin-kicin da fuska a wajen shagalin bikinsa

A wani labarin, wani ango ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayyana da fuska murtuk a wajen shagalin bikinsa.

An dai gano amarya tana kwasar rawa abin ta cike da farin ciki a wani bidiyo da ya yadu yayin da shi kuma ya tsaya kikam yana kallonta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel