Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wuse, Sun Halaka Mutum 1, Mutane da Yawa Sun yi Batan Dabo

Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wuse, Sun Halaka Mutum 1, Mutane da Yawa Sun yi Batan Dabo

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu gidaje dake yankin Wuse Zone 5 a babban birnin tarayyar Najeriya ta Abuja
  • Ganau ya tabbatar da cewa sun harba mutum biyu yayin da suka halaka mutum daya sannan wasu jama’ar ba a gan su ba
  • Ganau din yace wani tela mai suna Oshodi yana kwance a mace yayin da aka hanzarta mika wadanda aka harba asibiti duk da wani baya hayyacinsa

FCT, Abuja - ‘Yan bindiga a daren Talata sun kai farmaki wani gida kusa da tsauni a Unguwar Wuse Zone 5 dake Abuja inda suka harbi mutum 2 tare da halaka 1 yayin da mutane da yawa suka bace sakamakon gudun ceto rai.

‘Yan bindiga a Abuja
Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wuse, Sun Halaka Mutum 1, Mutane da Yawa Sun yi Batan Dabo. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wani ganau wanda ya tabbatarwa da jaridar Punch ta wayar salula, yace ‘yan bindigan sun dinga harbi babu kakkautawa a titin Amilomania inda daga bisani suka koma titin Toyin.

Yace:

“Mun ji harbi har sau biyu a yayin da suka fara dira wani gida a titin Amilonania. Yanzu haka suna titin Toyin a gidan karshe dake kusa da tsauni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Sun harbe wani tela mai suna Oshodi kuma yanzu haka kwance yake a mace. Sun harbi wani namiji amma mun kai shi asibiti a Phase 4 amma kuma baya cikin hayyacinsa.
“‘Yan bindigan sun tsere ta tsauni. Yanzu haka neman wasu jama’a muke yi kuma bamu gan su ba. Ta yuwu garkuwa aka yi dasu.”

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adey, bai dauka waya ba kuma bai yi martani kan sakon kar ta kwana da aka tura masa ba a daren Talata.

’Yan bindiga sun je har gida, sun sace basarake a Abuja

A wani labari na daban, wasu miyagun 'yan ta’adda a safiyar Lahadi, sun yi garkuwa da Dagacin Kuchibuyi, wani yanki mai nisa a ƙarƙashin yankin Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayyar Najeriya.

Wani shugaba a yankin, wanda ya zanta da Daily Trust, ya ce an yi awon gaba da Malam Isiyaka Dauda har cikin gidansa, wanda ke nesa da fadarsa yayin harin yan ta’addan.

A cewarsa, ‘yan bindiga kusan su 10 sun buɗe wuta sau biyu suna dira gidan, hakan ya ankarar da Yan sa'kai, inda ya ƙara da cewa tilas yan Sa'kai suka yi ta kansu yayin da masu garkuwan suka nufe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel