Sokoto: Buhari da Ministan Tsaro Suna Jihar, ‘Yan Bindiga Sun Halaka ‘Yan Sanda 3 da Wasu Mutum 3

Sokoto: Buhari da Ministan Tsaro Suna Jihar, ‘Yan Bindiga Sun Halaka ‘Yan Sanda 3 da Wasu Mutum 3

  • Yan ta’adda sun kai mugun farmaki kasuwar sati dake kauyen Yarbulutu, daidai lokacin da Shugaba Buhari da ministan tsaro ke jihar
  • Kamar yadda ganau suka bayyana, an halaka ‘yan sanda uku da suka zo kawo dauki tare da wasu ‘yan kasuwa uku dake hada-hadarsu
  • Ganau ya tabbatar da cewa, ‘yan bindigan sun bayyana a babura da makamai yayin da ‘yan sandan dake aiki suka hanzarta kawo dauki

Sokoto - ‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne a jiya da rana sun dira kasuwar Yarbulutu a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka halaka ‘yan sanda 3 da wasu ‘yan kasuwa 3, Daily Trust ta rahoto.

Shugaba Buhari
Sokoto: Buhari da Ministan Tsaro Suna Jihar, ‘Yan Bindiga Sun Halaka ‘Yan Sanda 3 da Wasu Mutum 3. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Farmakin ya faru ne wurin karfe 2:30 na rana yayin da Shugaba Muhammadu Buhari da ministan tsaro Salihi Magashi suke halartar taron COAS na shekara shekara.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Gano Wadanda Suka Kona Ofishin INEC, Asirin Masu Danyen Aikin Ya Tonu

Kamar yadda ganau ya bayyana, ‘yan bindigan da suka bayyana a babura sun budewa ‘yan kasuwa wuta, lamarin da yasa jama’a suka arce don gujewa salwantar rayukansu.

‘Yan sanda dake kan aikinsu kusa da wurin sun hanzarta zuwa kasuwar yayin da suka yi musayar wuta da ‘yan bindigan wanda hakan ya kawo kisan uku daga ciki yayin da aka kone motocin ‘yan sandan biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar yace rundunar ta samu rahoto kuma tuni suka fada aiki domin cafko maharan su fuskanci hukunci.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, wani mazaunin kauyen wanda ya ga yadda lamarin ya faru ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan bindigan ke addabar yankin a kowacce rana ba tare da an yi maganinsu ba.

Yace kananan hukumomin Sabon Birni da Isa a gabashin jihar Sokoto tuntuni ‘yan bindiga ke rike da su da masu garkuwa da mutane na jihar Zamfara da wasu sassan jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Ogun: Tsaka Tayi Ajalin Rayukan Mutum 6 ‘Yan Gida Daya Bayan Cin Abincin da ta Fada

“Ina da tabbacin wadannan ‘yan bindigan daga Zamfara suke kuma yanzu suka dawo yankinmu saboda iyaka da jihar da muke da ita ta gabas.”

- Ganau yace.

Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kai farmaki wani kauye a karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto inda suka halaka mutum shida.

Makamancin lamarin ya faru a shekarar da ta gabata inda wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne suka halaka mutum 40.

Yan sanda sun kama ‘yan bindiga 7, sun ceto mutum 15

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun damke ‘yan bindiga 7 bayan samamen da suka kai maboyarsu a kauyukan Anka.

Sun ceto wasu mutum 15 da miyagun suka yi garkuwa dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel