Wani Magidanci Ya Koka Kan Yadda Matarsa Ke Koransa Dag Gadon Sunnah Daga Haihuwa

Wani Magidanci Ya Koka Kan Yadda Matarsa Ke Koransa Dag Gadon Sunnah Daga Haihuwa

  • Wani mutumi ɗan Najeriya ya koka kan hana shi jin daɗin matarsa tun lokacin da Allah ya albarkace su da samun ƙaruwa
  • Da daddare ta hana shi kwanciya da ita a gado ɗaya, ta gwammace ta kwanta da ɗan jaririnsu, ta nemi ya koma wani wurin
  • Mutumin ya koma rokon karamin yaron ya tausaya masa ya koma ɗan karamin gadon yara da aka tanadar masa

Wani magidanci ya garzaya soshiyal Midiya ya koka kan babbar matsalar da yake fama da ita game da mai ɗakinsa a gida.

Mutumin ya bayyana cewa matarsa ta maida hankali kacokan kan ɗan da suka haifa kuma ya wallafa bidiyon abokiyar rayuwar tasa tare da yaron na kwance a gado.

Rigimar mata da miji.
Wani Magidanci Ya Koka Kan Yadda Matarsa Ke Koransa Dag Gadon Sunnah Daga Haihuwa Hoto: bigmiller09/TikTok
Asali: UGC

Wanda ya wallafa bidiyon a TikTok ya rubuta cewa:

"Amma wasu matan da gangan suke wa mazajensu haka domin su baƙanta musu rai."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An umarci Magidanci ya canza wurin kwanciya

Ya fara ɗaukar Bidiyon da nuna gadon wanda yaron ya maida wurin hutawarsa kana ya koka da halayyar matarsa na hana shi shigowa cikinsu a gadon aurensu.

Mutumin yace idan ta so zata maida yaron kan ɗan karamin gadonsa amma ta ƙi yin haka. Ya roki yaron ya tausaya masa ya koma kan gadonsa.

Matar, haifaffiyar ƙasar Ghana, an hangeta tana babbake sauran wurin da wani zai iya kwanciya a gadon da ɗayan hannunta don kar mijin ya hawo.

Kalli bidiyon anan

Jama'a sun maida martani

Davilekimmy yace:

"Ai da zaran ka haihu, gaba ɗaya soyayyar da matarka ke nuna maka zata koma kan jaririn, daga miji zaka koma Bestie."

Maggyhope yace:

"Ka jira har zuwa lokacin da matar zata haifi ɗiya mace, daga lokacim zaka gane danƙon alaƙar da take da yaron."

Winnerbabywinner8 tace:

"Ka sha romon jin daɗi a lokacinka dan haka ka bar yaro shi ma ya mori na shi lokacin."

Kwana Huɗu da Aure, Amarya Ta Kama Ango Na Saduwa da Yar Uwarta a Gado, Ta Turo Bidiyo

A wani labarin kuma Kwanaki hudu da ɗaura aure Amarya ta kama Sabon Angonta na kwanciya da yar uwarta a gadonsu

Lamarin ya sosa mata zuciyar har ta kai ga ta bar gidan ta kom Hotel tsawon mako ɗaya, babu wanka ba zuwa ko ina saboda bakin ciki.

Amaryar tace ba zata taɓa yafe musu ba don haka ta garkame lambobin iyayenta waɗanda suka fara rarrashinta ta yi hakuri, bidiyon lamarin ya girgiza mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel