An Gano Gawarwakin Jarirai 2 a Cikin Firij a Gidan Wata Mata a Kasar Faransa

An Gano Gawarwakin Jarirai 2 a Cikin Firij a Gidan Wata Mata a Kasar Faransa

  • An gano gawarwakin wasu jarirai a gidan wata mata, ana zargin ita ta kashe su ta boye a firij
  • ‘Yan sanda na ci gaba da bincike, an gano bugu a jikin daga cikin jariran da aka gano
  • Kasar Faransa na yawan fama da kashe-kashen kananan yara, musamman cikin shakrun baya-bayan nan

Faransa - An gano gawarwarkin jarirai guda biyu a cikin firij a gidan wata mata a Kudancin Faransa, ana tunanin ba mutuwa ce ta haka siddan suka yi ba, inji ‘yan sanda a ranar Litinin.

A cewar ‘yan sanda, bayan bincike an kama wata mata mai shekaru 41 da ake zargin tana hannu a lamarin kasancewar an tsinci gawarwakin yaran ne a cikin gidanta.

An gurfanar da matar a ranar Juma’a bisa zargin kisan kananan yara guda biyu, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsananin yunwa: Bidiyon mata 'yan Arewa na wawar shinkafa a kan tunkuya ya tada hankali

Ba a dai sani ba ko tabbatar da ita ce ta kashe wadannan yara guda biyu gaba dayansu mata ba.

An gano gawarwakin jarirai a firij
An Gano Gawarwakin Jarirai 2 a Cikin Firij a Gidan Wata Mata a Kasar Faransa | Hoto: Pascal GUYOT / AFP
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon binciken gawa

Binciken gawa da aka yi ya nuna daya daga cikin jariran ta sha bugu mai karfi, wanda ya kai ga rauni a jikinta, kuma ana kyautata zaton shi ya kashe ta.

Florence Galtier, jami’ar ‘yar sanda mai kula da lamarin ta ce, ba a dai san ciwon da jaririyar ta ji sakamako ne na duka ko faduwa ko rashin kula ko dai wani abu ba.

Ta kara da cewa, ba a kuma tabbatar ko jariran biyu tagwaye bane ba ko kuma dai watakila basu da alaka da juna, Khaleej Times ta tattaro.

A tun farko ‘yan sanda sun smau kira ne daga wani mutum da ba a gano bayanansa ba game da ajiye yaran a firij, wanda ake tunanin shi ma yana hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ce man fetur ba zai iya rike Najeriya, ya fadi mafita ga tattalin arziki

Ana yawan samun irin wadannan matsaloli sau tari a kasar Faransa, musamman cikin ‘yan shekarun nan.

A watan Maris din bana ne aka mata wata mata mai shekaru 30 bisa zargin adana yara biyu a cikin firij.

Haka nan a 2015, an samu faruwar irin wannan lamari, inda aka gano mutum biyar a cikin firij, lamarin da ya kai ga daure wata matashekaru 8 a gidan yari.

A Najeriya ma hakan ya faru, kwanakin baya aka tsinci gawar wata mata da aka bayyana batanta a jihar Kwara, lamarin da ya tada hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.