Man Fetur Ba Zai Iya Ciyar da Al’ummar Najeriya da Ke Kara Yawa Ba, Inji Tsohon Shugaba Obasanjo

Man Fetur Ba Zai Iya Ciyar da Al’ummar Najeriya da Ke Kara Yawa Ba, Inji Tsohon Shugaba Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce sam harkar man fetur ba zai iya riki Najeriya ba a nan gaba kadan
  • Ya bayyana bukatar a fara aikin inganta noma domin samar da wadataccen abinci da kuma daina dogaro da man fetur
  • Ya kuma bukaci ‘yan kasa da su tashi tare da mai da hankali ga noma, inda yace ta haka ne za a magance yawan ‘yan kasar

Abeokuta, jihar Ogun - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, man fetur da gas na kasar ba zai iya ci gaba da ciyar da al’ummar da ke kara yawa ba.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a karshen mako yayn da shugabannin kungiyar kabilar Tiv ta Mzough U Tiv (MUT) a dakin karanatunsa da ke cikin gidansa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Qatar ta fi Ingila dadi: Matan turawa sun ce hana shan barasa a 'World Cup' ya sa ba a hantararsu

A cewarsa, noma da kasuwancin kayayyakin gona ne kadai zai iya magance karuwar adadi na ‘yan kasar a halin da ake ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Obasanjo ya magantu kan halin tattalin arzikin kasar nan
Man Fetur Ba Zai Iya Ciyar da Al’ummar Najeriya da Ke Kara Yawa Ba, Inji Tsohon Shugaba Obasanjo | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Inda ya kamata a mai da hankali ga tattarin arzikin kasar nan

Ya yi kira ga jama’a da su mai da hankalinsu ga fannin noma a matsayin madadi ga fannin mai da tattalin arzikin kasar ya dogara dashi a yanzu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Idan Najeriya na son komawa kan daidai, zaben 2023 ya kamata ya zama mafarin canji.”

Kabilar Tiv ta ba Obasanjo matsayin “Babban Mayaki”, inda ta siffanta gwagwarmayarsa da abin da kasar nan ke bukata, rahoton Vanguard.

A tun farko, shugaban kungiyar ta Tiv, Cif Iorbee Ihagh ya bukaci tsohon shugaban kasan da ya sa hannu wajen kawo kamfanin matse ‘ya’yan itatuwa a jihar Benue.

Kara karanta wannan

2023: Malamin addini ya fadi ta yadda shugaban Najeriya na gaba ya kamata ya fito

Hakazalika, ya bukaci Obansanjo ya sa baki a siyasar kasar nan tare da dakile hare-haren makiyaya kan lardin Tiv da dai sauran batutuwa.

Ana yawan samun rikici tsakanin kabilar Tiv da Fulani makiyaya a jihar Benue, lamarin da ke kara jawo cece-kuce a kasar nan.

Rikicin makiyaya da manoma ya kai ga mutuwar mutane a Borno

A wani labarin, kunji yadda rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jiahr Borno, inda mutane 8 suka mutu.

An kuma kone gidaje sama da 47 a yankin na Borno duk dai saboda rikicin da ya barke tsakani.

Hukumomin gwamnati sun zauna don tattaunawa da kawo mafita mai dorewa ga karuwar rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel