Bidiyon ’Yan Matan Arewa Na Wawar Shinkafa a Gidan Biki Ya Girgiza Intanet

Bidiyon ’Yan Matan Arewa Na Wawar Shinkafa a Gidan Biki Ya Girgiza Intanet

  • Wasu mata sun ba da mamaki a kafar sada zumunta yayin da aka ga suna wawar shinkafa a kan tukunya tun kafin a sauke
  • Wannan lamari da alamu ya faru ne a gidan biki, domin mata ne tare da yawa suna kokarin kwasar shinkafar
  • Jama'a da dama a Twitter sun shiga mamakin halin da kasar nan ke ciki, yayin da wasu ke kallon lamarin na da alaka da dabi'ar matan

Wani bidiyo mai ban mamaki ya nuna lokacin da wasu mata ke kokuwar kwasar shinkafa a tukunya a wani wurin da ya yi kama da gidan biki a cikin wani gida.

A bidiyon da sanata Shehu Sani ya yada a shafinsa na Twitter, an ga lokacin da matan ke rike da kwanuka da robobin zuba abinci, inda kowace mace ke kokarin ta ga ta samu rabinta.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kama Mijinta Na Rage Zafi Da Wata Yar Magajiya, Bidiyon Matakin da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane

A ciki kuma, an ji wata mata na salati tare da ta’ajibin abin da ya faru yayin da sauran matan da ke kan kokarin ke ci gaba da wawar shinkafa ko a jikinsu.

Matan Arewa na wawar shinkafa a gidan biki
Bidiyon 'yan matan Arewa na wawar shinkafa a gidan biki ya girgiza intanet | Hoto: @ShehuSani
Asali: UGC

A rubutun da ya yada dauke da bidiyon, Shehu Sani ya tambaya cewa, ina dalar buhunnan shinkafa da gwmanatin Najeriya ta yi bikin nunawa a tsakiyar shekaran nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta cewa:

“A ina dalar shinkafar take?”

Kali bidiyon:

Idan baku manta ba, gwamnatin Najeriya na ci gaba da nunawa duniya akwai wadataccen abinci a kasar, duk da kuwa ‘yan kasar na fama da matsanancin yunwa da fatara, wanda hukumar kididdiga ta tabbatar da hakan.

Martanin jama’a a Twitter

Bayan ganin wannan bidiyo, mutane da dama sun shiga mamakin yadda wannan lamari ya faru a wurin matan da aka ga sun yi kama da ‘yan Arewa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ce man fetur ba zai iya rike Najeriya, ya fadi mafita ga tattalin arziki

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

@UnlimitedEniola yace:

"Su wadannan mutanen su za su je su zabi wadanan shugabannin. Mutanenmu na bukatar wayar da kai."

@excellency_jr yace:

" Baba buhari na aiki."

@Shuaib2110 yace:

"Baka ji kunyar yada wannan ba....?
"Malam wadannan mutane mutanenka ne fa.."

@ashkassope yace:

"Shin batu na dalar shinkafa ko kuma hali, idan da sun bi layi mai sauki da ya ishi kowa."

@Jasperson4190 yace:

"Kai....Ina tausayawa kasa ta abar kaunata, akwai tsananin yunwa a kasar nan...2023 wata dama ce gare mu mu sake rubuta kura-kuranmu na baya."

@collinsweglobe yace:

"Yanzu ta yaya za ka yiwa wadannan mutanen nasihar kada su zabi shugaba dan rashawa idan ya basu 5k?"

A baya tsohon shugaban kasa a Najeriya ya ba da shawarin a kama hanyar noma, harkar man fetur ba za ta ci gaba da ciyar da kasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel