Ali ya ga Ali: Ganduje da Jafar Jafar Sun yi Kicibus a Landan, Sun Gaisa a Bidiyo

Ali ya ga Ali: Ganduje da Jafar Jafar Sun yi Kicibus a Landan, Sun Gaisa a Bidiyo

  • Dan jarida Jafar Jafar ya ci karo da Gwamna Ganduje a birnin Landan bayan shekaru da barinsa kasar
  • Fitaccen ‘dan jaridar ya fitar da bidiyoyin Gwamnan yana sankama daloli a babbar riga wanda ya karba daga ‘yan kwangila
  • Sun hadu a farfajiyar Gidan Chatham dake Landan inda suka sha hannu tare da kashewa suna dariya ga juna

Landan - Fitaccen ‘dan jarida kuma mamallakin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar, yayi kicibus da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a London ranar Litinin.

A shekarar 2018, kafar Jafar ta wallafa bidiyoyin gwamnan inda ake zargin yana karbar cin hanci daga ‘dan kwangila, lamarin da Gwamnan ya musanta inda yace hada bidiyoyin aka yi.

Bai tsaya nan ba, ya shigar da kara kan sunansa da mawallafin ya bata inda yake bukatar a biya shi diyyar N3 biliyan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ga Atiku: Ka Zabtare Kudin Makaranta a Jami’arka ko ‘Yan Najeriya da Halarta

‘Dan jaridar ya fara buya inda daga bisani ya bar Najeriya kan zargin barazana da ake masa ga rayuwarsa.

Amma a ranar Litinin, su biyun sun ci karo a farfajiyar gidan Chatham inda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC yayi jawabi.

A gajeren bidiyon da mawallafin ya fitar a shafinsa na. Facebook , su biyun sun gaisa inda suka sha hannu tare da yi wa juna dariya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karin bayani na nan tafe…

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng