Kwankwaso ga Atiku: Ka Taimaka ka Rage Kudin Makaranta a Jami’arka Ko don Magoya Bayanka

Kwankwaso ga Atiku: Ka Taimaka ka Rage Kudin Makaranta a Jami’arka Ko don Magoya Bayanka

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya roki Atiku da ya rage kudin makaranta a jami’arsa
  • A cewar Kwankwaso, idan Atiku ya rage yawan kudin makarantar, dubban ‘yan Najeriya magoya bayansa zasu samu damar samun ilimi
  • Atiku a bangarensa ya jaddada amfanin ilimantar da yara yadda ya dace, wanda yace da kansu zasu dawo su habaka bangaren ilimi tare da kawo cigaban tattalin arziki

FCT, Abuja - ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Lahadi yayi kira ga takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya rage kudin makarantar jami’arsa dake Najeriya.

Tattaunawa da ‘yan takara
Kwankwaso ga Atiku: Ka Taimaka ka Rage Kudin Makaranta a Jami’arka Ko don Magoya Bayanka. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Atiku ne ya kafa jami’ar Amurka dake Najeriya a garin Yola dake jihar Adamawa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kwankwaso yayi wannan tsokacin ne yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda za a inganta bangaren ilimi a wani taron da Arise TV ta gayyacesu tare da hadin guiwar cibiyar damokaradiyya da cigaba da jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Lugude da Gurfana a Kotu, Dalibin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Dole ne inyi godiya ga Waziri, yana da jami’a wacce take da kyau sosai. Abu daya da ya dace yayi kokarin yi shi ne ya yi kasa da kudin makarantar ta yadda magoya bayansa da ‘yan Najeriya masu yawa zasu iya shiga.”

Kwankwaso ya kara da cewa, zai karfafa bangarori masu zaman kansu da su zuba hannayen jari a fannin ilimi tun daga firamare har zuwa jami’a yayin da yace komai dangane da ASUU dole ne ya zamo na gaskiya.

A yayin amsa tambayar, Atiku ya tsaya kan cewa ilimi yafi komai amfani cikin abubuwan da ya dace yara su samu ta yadda za a habaka cigaban kasa yayin da ya jaddada cewa a zuba kudi masu yawa a bangaren ilimi.

A kalamansa:

“Abu mafi muhimmanci shi ne a ilimantar da yaranmu. Kuma ba ilimi kawai ba, yadda ya dace. Daga nan ne zasu iya bada gudumawa a fannin cigaban bangaren wanda shi ne tushen tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Subut da baka: Tinubu ya sake yin wata katobarar da ta fi ta baya, 'yan Najeriya sun girgiza

Atiku ya kara da bada misali kan yadda aka kirkiro UBEC yayin da yake mataimakin shugaban kasa wanda ya zama wajibi ga kowanne yaro ‘dan Najeriya da ya samu ilimin fura are zuwa karamar sakandare kyauta.

Kwankwaso ya koma makaranta, ya kammala digirin digirgir a India

A wani labari na daban, Sanata Rabiu Kwankwaso Kwankwaso ya kammala digirin digirgir daga wata jami’ a kasar India.

Tsohon Gwamnan ya kammala karatun ne daga jami’ar Sharda dake Indiya kan Injiniyancin ruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel