Bayan Sa’o’i Kadan da Mubaya’a ga Sabon Khalifa, Sojoji Sun Halaka ‘Yan ISWAP

Bayan Sa’o’i Kadan da Mubaya’a ga Sabon Khalifa, Sojoji Sun Halaka ‘Yan ISWAP

  • Zakakuran sojin Najeriya sun yi nasarar halaka mayakan ISWAP masu tarin yawa a farmakin da suka kai kan sojin a garin Damboa na Borno
  • Sun kai hari kan sojojin bayan sa’o’i kadan da yin mubaya’a ga Abu al-Hussein al-Quraishi matsayin sabon shugaban kungiyar ISIS
  • Mayakan sun bayyana a motocin yaki da wasu motocin Hilux dauke da bindigogin harbo jirage amma sojin suka yi musu kwantan bauna tare da gamawa su

Borno - Dakarun sojin Najeriya sun halaka wasu mayakan ta’addancin ISWAP bayan musayar wuta da suka yi a garin Damboa dake jihar Borno.

‘Yan ta’addan ISWAP
Bayan Sa’o’i Kadan da Mubaya’a ga Sabon Khalifa, Sojoji Sun Halaka ‘Yan ISWAP. Hoto daga @Zagazolamakama
Asali: Twitter

Kamar yadda Zagazola Makama, wata wallafa da ta mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi ta bayyana, ‘yan ta’addan sun kaddamar da farmaki a garin Wajiroko dake jihar Borno.

Farmakin ya faru ne bayan sa’o’i kadan da ‘yan ta’addan suka yi mubaya’a ga Abu al-Hussein al-Qurashi a matsayin sabon shugaban ISIS.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 15, Sun Kama ‘Yan Bindiga 7

“An tattaro cewa, ‘yan ta’addan da ba a iya kayyade su ne suka kai farmakin garin Wajiroko a motocin yaki biyu a Hilux shida dauke da bindigogin harbo jirgin sama.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Rahoton yace.

“Wata majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama cewa, ‘yan ta’addan sun fara harba and bama-bamai yankin Gubub kafin su biye baya da farmakin.
“Jajirtattun sojojin sun tsaya tare da musayar wuta da ‘yan ta’addan wanda aka kwashe kusan mintuna 40 ana yi.
“Daga bisani dole ta sa ‘yan ta’addan suka tsere tare da barin wurin duka da miyagun raunika.
“Sai dai a rashin sanin ‘yan ta’addan da suka arce, an sake turo dakaru daga Sabon Gari da Damboa karkashin jagorancin Birgediya Janar B. O Omolariola, kwamandan birged na 25 wanda tuni suka yi kwantan bauna ga ‘yan ta’addan a hanyarsu ta wucewa.

Kara karanta wannan

Yadda iPhone 7 Ta Jawo Jami’an Tsaro Suka Kamo Wanda Ya Ci Mutuncin Aisha Buhari

“Wannan kwantan bauna kuwa yayi amfani tunda an halaka ‘yan ta’addan tare da tarwatsa motocin su na yaki biyu dake dauke da mayaka.”

- Rahoton yace.

Kayayyakin da aka samo daga wurin ‘yan ta’addan sun hada da: bindigar kirar FN guda daga, AK47 guda biyu, bindiga harbo jirgin sama daya, gurneti 35, harsasai da sauransu.

Yan sanda sun ceto mutum 15, an damke ‘yan ta’adda 7

A wani labari na daban, ‘yan sanda sun ceto wasu mutum 15 da aka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara.

Ba su tsaya nan ba, ‘yan ta’adda 7 a jihar Zamfara bayan samamen da suka kai maboyar ‘yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel