Gwamnatin Tarayya Na Shirin Sanya Haraji Akan Hada Hadar Kudade ta Intanet

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Sanya Haraji Akan Hada Hadar Kudade ta Intanet

  • Majalissar Kula Da Tattalin Arzikin Kasa (NEC), Ta Mika Kudirin Doka Gaban Hukumar Zartarwa Kasa (FEC) kan Sake Fasalin Dokokin Kudi
  • Ministar Kudi Da Kasafi A Nigeria Ta Sanar Da Aike Sabon Daftarin Tsarin Dokokin Zuba Hanun Jari Na Shekarar 2023
  • A Tsakiyar Watan Da Ya Gabata Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Kudaden Da Yan Kasar Zasu Ringa Amfani Da Su

Abuja: Zainab Ahmed wacce take ministar kudi da kasafi ta ce akwai tanadin haraji akan kudaden cryptocurrency da sauran hada-hadar kudi a cikin kudirin sake fasalin dokokin kudi na 2022. A wata sanarwa da Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fitar, yace ministar ta bayyanwa majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) abinda kudirin ya kunsa a taro majalissar na musamman da aka yi ranar Alhamis din nan. Jaridar The Cable ta rawaito cewa ministan ta ce kudurin dokar da za'a gabatarwa majalissa an dora ta ne kan wasu tsare-tsare guda biyar. Ta ce tsarin dokokin da ake son gabatarwa din akan haraji zasu samar da ayyukan yi, haɓakar tattalin arziki, da kuma sake fasalin yadda ake samun kudin shiga a Nigeria da yadda ake tassarufi da su.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Litinin Din Nan Mai Zuwa Dalbai Zasu Far Zanga-Zanga Dan A Saki Aminu

Ministan kudi
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Sanya Haraji Akan Hada Hadar Kudade ta Intanet Hoto: TheCable
Asali: UGC

Ta ce kudurin dokar ya nemi yin gyara kan kudaden shiga da kuma ka’idojin karbar haraji da kuma wasu sauye-sauyen akan habaka tattalin arziki.

Zainab tace kudirin yana nufin yin gyara da kuma tanadin dokoki dangane da yadda ake tafiyar da harkokin kudi na gwamnatin tarayya.

"Alal misali, a ƙarƙashin ginshiƙin kudin Harajin, za a shigar da dukkan sassan tattalin arzikin cikin, kamar wanda suka haɗa da Harajin Samar da Kuɗi daga cinikaiyar yana gizo da kuma hada-hadar kudi na cryptocurrency,"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hakazalika, a karkashin dokar akwai kudirin doka kan bangaren hakar iskar gas da kuma rage kudin shiga daga fitar da iskar da ake yi"

Karƙashin kudirin da kuma gyare-gyare dokokin harajin za a lamunin zuba hannun jari; canje-canje wajen habaka hakar mu'amalar kudin kasashen waje da kuma inganta yanayin kudin kasa

Ministan ta ce kudirin da za'a gabatar zai fayyace harajin cryptocurrency da sauran nau'oinsa a karkashin manufofin gwamnati na bunkasa harkar harajin kasa da bunkasa kasuwancinzamani wanda akeyi a intanet.

Kara karanta wannan

Sojin Nigeria Sunyi Nasarar Kashe Shugaban ISAWP A Nigeria, Bayan Wani Hari Da Suka Kai

Mai Gwamnoni Suka Ce Game da Batun Harajin

Bayan jawabin ministar, gwamnonin jihohin Sokoto, Borno, Kaduna, Kebbi da Ogun da dai sauransu sun yi tsokaci kan kudirin dokar. Bayan tsokaci nasu, majalissar ta yanke shawarar sabunta daftarin kudirin dokar tare da samun karin bayanai daga gwamnonin jihohi yayin da kudirin ke gaban majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) kafin shugaban kasa ya aika da shi zuwa ga majalisar dokokin kasar.

Baban Bankin Nigeria Ya Umarci Rufe Asusun Masu Amfani da Kudin Crypto

A cikin 2021, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan da su rufe asusun mutane ko hukumomin da ke da hannu a hada-hadar kudin cryptocurrency. Babban bankin ya kara yin kira ga 'yan kasar da su guji mu'amala da kudin crypto , yana mai gargadin cewa amfani da su din wata haramtacciyar harkar mu'amala kudi ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel