Kudin Intanet: Babban Bankin Najeriya CBN ya haramta kasuwancin Bitcoin
- Babban bankin Najeriya ya sake jaddada haramcin ta'ammuli da kudadden yanar gizo
- Babban bankin ya bayyana ta'ammuli da kudaden a matsayin hadari a fanninkasuwanci
- Hakazalika babban bankin ya bayyana rashin iya bin diddigin kudaden daga cikin dalilan haramcin
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya baiwa bankunan Najeriya umarnin rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kudin yanar gizo na cryptocurrency, matakin da bai yi wa dubban 'yan Najeriya dadi ba, BBC Hausa ta ruwaito.
Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a ga bankunan hada-hadar kudi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kudi ba (NBFI) da kuma sauran ma'aikatun harkokin kudi a kasar.
"Kari a kan umarnin da aka bayar tun a baya, bankin (CBN) yana tunatar da ma'aikatun da ke mu'amala da kudaden yanar gizo ko kuma dillalansu cewa haramun ne," inji sanarwar.
KU KARANTA: 'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci
A shekara ta 2017, CBN ta ce kudaden yanar gizo irin su bitcoin da litecoin da sauransu ana amfani da su ne wurin daukar nauyin ta'addanci da kuma halasta kudin haramun, ganin cewa ba a iya bibiyar tushe ko sawunsu.
"Saboda haka, an umarci dukkanin NBFIs, NBFIs da OFIs da su tantance mutanen da ke amfani da irin wadannan kudade sannan su rufe asusun ajiyarsu," in ji umarnin.
Hakazalika a shekara ta 2018, CBN ta ce kudaden ba sa cikin abubuwan da mai su zai iya kai kara kotu idan yana neman hakkinsa a Najeriya.
Wannan yake nuna irin hadari dake cikin ta'ammuli da irin wadannan kudade na yanar gizo a kasar ta Najeriya.
KU KARANTA: An kama wasu mutane huɗu da laifin noman tabar wiwi a jihar Ondo
Jerin kuɗin yanar gizo da ake kasuwanci da su
Bitcoin
Ethereum (ETH)
Litecoin (LTC)
Cardano (ADA)
Polkadot (DOT)
Bitcoin Cash (BCH)
Stellar (XLM)
Chainlink
Binance Coin (BNB)
A wani labarin, Wata jami’a a Babban Bankin Duniya bangaren Tattalin Arziki mai suna Gloria Joseph Raji ta bayyana wa duniya cewa annobar cutar COVID-19 nakasa tattalin arzikin Najeriya.
Najeriya a halin yanzu na fuskantar mummunan yanayi na tallalin arziki da ba ta jima bata fuskanta ba tun shekarar 1980, in ji jaridar Punch.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng