Shugaban ISWAP Muhammad Malik Ya Sheka Lahira A Wani Bata Kashi Da Akai Tsakaninsa da Sojojin Nigeria

Shugaban ISWAP Muhammad Malik Ya Sheka Lahira A Wani Bata Kashi Da Akai Tsakaninsa da Sojojin Nigeria

  • Wani Harin Sojoji Ya Kashe Babban Shugaban ISWAP na yankin Tafkin Chadi Muhammed Malik, Da Wasu kwamandojinsa
  • Har Yanzu Ana Samun Hare-Haren Kungiyar masu ikirarin yin Jihadi A Nahiyar Yammacin Afrika
  • A shekarar da ta gabata ne dai shugaban Kungiyar Boko Haram Muhammad Shekau Ya riga Mu gidan Gaskiya Sakamakon Kashe kansa da yayi

Barno: Wani hari da dakarun sojin sama da sojojin Operation Hadin Kai suka kai, ya yi nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar ta'addanci ta yankin yammacin Afirka, Muhammed Malk, wanda ke muba'ya'a ga ISWAP

Runduna ta musamman ce tare da hadin kan sashin leken asiri na sojojin sama da na kasa karkashin jagorancin sojojin Najeriya su kai harin da jirgin ta mai kirar Super Tukano a karkashin yunkurin kawar da ikirarin masu rajin jihadi.

Majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama, cewa Muhammed Malik ya rasu ne a ranar 29 ga watan Nuwamba, sakamakon munanan raunukan da ya samu yayin harin.

ISWAP
Shugaban ISWAP Muhammad Malik Ya Riga Mu Gidan Gaskiya A Wani Bata Kashi Da Akai Hoto: The Guardian
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Muhammad Malik

Muhammed Malik yana cikin manyan jagororin ISWAP kuma ya taba zama memba a Majalisar Shura a Marte kafin ya tafi kwas kan Injiniyan Kwamfuta da Samar da abubuwan fashewa, wanda ISIS ke daukar nauyin yi a Somaliya.

Majiyar ta ce mutuwar Malik wata dama ce da za'a iya cewa an samu lagon kungiyar ta ISWAP, yayin da take ci gaba da yin asarar manyan jagororinta da kuma karfafawa dakarun Operation Hadin Kai da Multi- JTF gwuiwa (MNJTF).

Majiyar ta bayyana cewa babu wani tabbaci daga bangaren yada labarai na kungiyar IS, wanda galibi ke saurin kai hare-hare da yada bayananta don tabbatar da mutuwar shugabanninta.

Zagazola ta fahimci cewa akalla jiragen ruwa guda biyar dauke da jagororin kungiya da kuma wadanda suke biyayya ga jagorancin tafiyar malik ne suka rasa ransu a harin

Haka nan kuma majiyar tace wasu mayaka daga yankin Bakkassi a kasar Kamaru sun isa Sabon Tumbu domin gudanar da addu’o’in wadanda suka mutu.

Shekau Ya Rasa Ransa A Dalilin Tashin Bam

Kungiyar ISWAP mai ikirarin kafa daular Islama, wacce ta balle daga kungiyar Boko Haram, ta tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau, tsohon shugaban kungiyar Boko Haram.

Wani rahoton sirri na ‘yan sanda da aka ba TheCable ya ambato wasu manyan kwamandojin ISWAP suna cewa Shekau ya tarwatsa kansa da kansa a ranar 19 ga Mayu bayan arangama da 'yan ta'addan ISWAP.

An ce shugaban na Boko Haram ya kashe kansa ne da bam "lokacin da ya lura cewa mayakan ISWAP na son kama shi da ransa".

Asali: Legit.ng

Online view pixel