Mijina ba Shine Uban ‘Da na Ba, Amma Ban Taba Kwanciya da Wani ba, Matar Aure ta Koka

Mijina ba Shine Uban ‘Da na Ba, Amma Ban Taba Kwanciya da Wani ba, Matar Aure ta Koka

  • Wata matar aure ta matukar fusata kan sakamakon gwajin kwayar halitta da tayi wa daya daga cikin ‘ya’yanta wanda ta kasa gane dabi’arsa
  • Matar ta yanke hukuncin gin gwajin ne domin ta sha waye mahaifin yaron, amma sakamakon ya nuna cewa ba ‘dan mijinta bane
  • Wani David Bonbze-Mbir ne ya wallafa labarin Matar a shafinsa Na Facebook kuma hakan yasa jama’a sun dinga gurzar kwakwalwarsu don gano bakin zaren

Labarin wata mata wacce ta musanta kwanciya da wani namiji wanda ba mijinta ba ya bazu a dandalin sada zumuntar zamani na Facebook.

Matar aure
Mijina ba Shine Uban ‘Da na Ba, Amma Ban Taba Kwanciya da Wani ba, Matar Aure ta Koka. Hoto daga David Bonbze Mbir
Asali: Facebook

Labarin mai bada mamaki an wallafa shi ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba a shafin wani David Bonbze-Mbir, wanda yace daya daga cikin ‘ya’yan matar ba na mijinta bane.

A labarin, David yace matar ta zanta da shi kan sakamakon gwajin kwayar halittan da tayi wa daya daga cikin ‘ya’yanta.

Kara karanta wannan

Daliban Makarantar Sakandare Sun Gabatarwa Malaminsu Kyautar Tsumagiya a Wurin Aurensa a Bidiyo

Sakamakon gwajin DNA ya harzuka matar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwajin kamar yadda tace, ya zama dole ganin cewa yaron yana da dabi’a ta daban da sauran yaranta.

Sakamakon gwajin kuwa da ya harzuka matar ya nuna cewa ba mijinta bane uban yaron.

Ban taba kwanciya da wani namiji ba

Amma kuma abun mamakin shi ne, matar ta musanta taba kwanciya da wani mutum baya da mijinta.

A karshen labarin, David yace:

“Saboda mijinta ne namiji daya tilo da ta kasance da shi tun bayan haduwarsu, ta kasa yadda cewa Sakamakon gwajin nan daidai ne kuma ta yaya hakan ta faru.
“Babu wanda zai yarda cewa bata taba kasancewa da wani namiji ba tun bayan haduwarta da mijinta. Ta samu cikin yaron ta yuwu bayan ta auri mijinta amma da wani.”

Jama’a sun dinga wasa kwakwalwa a sashen tsokaci

Kara karanta wannan

Abinda 'Yan Siyasar Mu Na Arewa Zasu Koya Daga 'Yan Kudu, Aisha Buhari

Ana wallafa labarin, jama’a da yawa sun dire a kan ta. A halin yanzu, ta samu jinjina sama da 800 tare da tsokaci sama da 1800.

Ga wasu daga cikin tsokacin:

Vincentia Nutakor yace:

“Asibitoci suna tafka kuskure cike da takaici.”

Pascaline Adamu Kori tace:

“Ko dai musayar yaron aka yi mata?”

Mavis Agbedziw yace:

“‘Dan ba nata bane kuwa.”

Eva Akpablah yace:

“Ba zai yuwu ba, tabbas wani abu ne ba daidai ba ya faru.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel