Bidiyon Daliban Sakandare Suna Gabatarwa Malaminsu Kyautar Bulala a Wurin Shagalin Aurensa

Bidiyon Daliban Sakandare Suna Gabatarwa Malaminsu Kyautar Bulala a Wurin Shagalin Aurensa

  • A wani shagalin aure da aka yi a baya-bayan nan a jihar Imo, wasu daliban makarantar sakandare sun bai wa malaminsu kyautar bulala
  • Kyautar mai bada mamaki an karbeta ne ta hannun mai jawabi a wurin bikin wanda a bayyane ya dinga mamakin abinda malamin zai yi da tsumagiyar
  • Bakin da suka halarci wurin bikin sun saki baki kan wannan kyautar da daliban suka yi wa malaminsu a wannan babbar ranar ta rayuwarsa

An yi kwarya-kwaryar dirama a wurin wani shagalin aure a jihar Imo bayan tawagar wasu daliban makarantar sakandare sun gwangwaje malaminsu da kyautar bulala.

Daliban sakandare
Bidiyon Daliban Sakandare Suna Gabatarwa Malaminsu Kyautar Bulala a Wurin Shagalin Aurensa. Hoto daga @official_mc_freedom
Asali: UGC

Daliban masu abun mamaki sun bayyana da bulala tilo guda daya kuma suka mika ta ga mai jawabi a wurin bikin wanda hakan ya bai wa bakin dake zaune mamaki.

A bidiyon TikTok din, MC din ya tambaya hikimar bayar da wannan kyautar da kuma abinda suke tsammanin angon wanda shi ne malaminsu zai yi da ita.

Bakin dake zazzaune sun sheke da dariya yayin da MC din ya fara tuhumar yaran.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da Legit.ng ta tuntubi mai jawabi a wurin taron mai suna Achinike Freedom, ya sanar da cewa tabbas lamarin ya faru a wani biki da ya jagoranta a yankin bankin duniya dake jihar a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba.

Duk da bai iya gane wacce makaranta ko kuma wanne darasi malamin ke koyarwa ba, ya sanar da cewa sunan angon shi ne Fasto Abuchi.

Da aka tambaye shi yadda malamin ya karba wannan kyautar bada mamakin, Freedom yace:

“Dariya kawai ya dinga yi.”

Kalla bidiyon a kasa:

Hotunan daliban sakandare zaune a kasa suna rubutu a aji

A wani labari na daban, wasu hotunan daliban makarantar sakandare zaune kasa dirshan suna rubutu a aji ya janyo cece-kuce.

A wallafar da wani lauya mai suna Festus yayi, Yace daliban wata makarantar Sakandare ne dake jihar Ogun kuma tana nan wurin Watarsided dake Iwopi.

Lauyan yace daliban makarantar St.Kizitos ne kuma a nan jarabawa suke rubuta wannan, hakan ya faru ne sakamakon halin ko in kula da gwamnatin jihar ta nuna wa bangaren ilimi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel