Bauchi: Matashi ya Sheke Abokinsa Don yaki Siya Masa Barasa

Bauchi: Matashi ya Sheke Abokinsa Don yaki Siya Masa Barasa

  • Wani matashi mai shekaru 29 ya fada komar ‘yan sanda sakamakon halaka abokinsa da yayi a gidan shan barasa dake Dass a Bauchi
  • An gano cewa Monday ya je gidan da dare inda ya tarar da Abdulrazak tare da abokai suna shan giya, ya bukaci ya siya masa amma ya ki
  • Monday ya bibiyi Abdulrazak har hanyar tafiyarsa gida inda yayi amfani da kahon dabba ya soka masa a wuya wanda hakan yayi ajalinsa

Dass, Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tace ta kama wani matashi mai shekaru 29 wanda ake zargin ya sokawa wani mutum mai shekaru 30 wuka har ya mutu saboda ya ki siya masa barasa, jaridar Punch ta rahoto.

Taswirar Bauchi
Bauchi: Matashi ya Sheke Abokinsa Don yaki Siya Masa Barasa. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, yace lamarin ya faru a ranar 17 ga watan Nuwamban 2022 a wani wurin shan giya dake kauyen Bagel na karamar hukumar Dass ta jihar Bauchi.

“Rundunar ta kama wani Monday Ajasco mai shekaru 29 a Kafin Tafawa Bauchi a ranar 17 ga watan Nuwamban 2022 bayan ta samu bayani kan hannunsa dake cikin kisan wani.
“Binciken da aka yi ya bayyana cewa a ranar 16 ga watan Nuwamban 2022 wurin karfe 11 na dare, wanda ake zargi mai suna Monday ya je gidan giya dake kauyen Bagel a karamar hukumar Dass inda ya hadu da wani Abdulrazak Ibrahim mai shekaru 30 tare da wasu suna shan barasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wanda ake zargin ya bukaci Abdulrazak da ya siya masa barasa amma mamacin ya ki.
“Wannan cigaban ya kawo tashin hankali tsakaninsu kuma wanda ake zargin bai ji dadi ba. Bayan wani lokaci, sun yanke hukuncin barin gidan giyan don su tafi gida yayin da wanda lamarin ya ritsa dasu ya tafi kafin su.

“Abokin mamacin ya ji ihu daga abokinsa amma daga nesa. Bayan isa wurin, ya samu abokinsa kwance a jini yayin da wanda ake zargin ke tsaye kusa da shi rike da kahon dabba. Ya kara da barazanar sokawa abokin wuka yayin da ya tambaye shi daliinsa na yin hakan.
“Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya bibiya tare da harar wanda ya mutu da kahon da ba a wuyansa.
“A sakamakon haka, ya samu miyagun raunika inda aka hanzarta mika shi babban asibitin Dass amma aka tabbatar da mutuwarsa.”

- Yace.

Ya bayyana cewa, za a mika wanda ake zargin gaban kotu domin hukunci bayan kammala bincike.

Aboki ya halaka abokinsa saboda N100

A wani labari na daban, wani matashi mai suna Emma ya sokawa abokinsa mai suna White Lion wuka a kan N100 a Legas.

Lamarin ya faru wurin karfe 11 na dare a yankin Apapa dake jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel