Majiya: 'Yan Sanda Sun Kwamushe Dalibin da Yace Aisha Buhari Ta Ci Kudin Talakawan Najeriya

Majiya: 'Yan Sanda Sun Kwamushe Dalibin da Yace Aisha Buhari Ta Ci Kudin Talakawan Najeriya

  • Wani matashi ya gamu da fushin hukuma bayan da aka kama shi bisa zargin ya cin zarafin uwar gidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari
  • A watan Yuni ne matashin dan Arewa mai suna Aminu Muhammad ya yi wani rubutu mai cike da gatsali kan uwar gidan shugaban kasan
  • An taba kama wasu matasa a Kano bisa irin wannan laifi, an yanke musu hukuncin bulala 20 kowannensu da kuma share harabar kotu

Najeriya - ‘Yan sanda sun kama wani matashin dan jami'a, Aminu Muhammad bisa laifin yin rubutun suka ga uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, inji rahoton TheCable.

Rubutun da matashin ya yi a Twitter a watan Yunin 2022 ya ce:

“Su mama anchi kudin talkawa ankoshi.”

Rubutun da ya yada dai na dauke da hoton uwar gidan shugaban kasa, lamarin da ake kyautata zaton shi ya kai ga kame matashin kwanan nan.

Kara karanta wannan

An Kona Gidan Jigon PDP Awa 24 Bayan Gwamna Ya Masa Kyautar Sabuwar Mota A Babban Jihar Arewa

An kama matashin da ya ci zarafin Aisha Buhari
Majiya: 'Yan sanda sun kwamushe dalibin da ya ce Aisha Buhari ta ci kudin talakawa | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda aka kamo shi

An ruwaito cewa, hukumar DSS ta kama Aminu ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, sai dai wasu majiyoyi masu karfi sun ce ‘yan sanda ne suka kama shi.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, Aminu ya kasance dalibin aji biyar a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa.

Ya zuwa yanzu dai ba a san ko an ba matashin damar ganawa da iyalansa ba ko kuma samun damar ganawa da lauya.

Jaridar People Gazette ta bayyana cewa, matashin ya sha lakada daga jami'an tsaron a lokacin da suka kama shi da misalin karfe 12 na rana.

Muyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sanda bai amsa duk wasu kiraye-kiraye da aka yi masa kan lamarin ba.

Ba wannan ne karon farko da ake hukunta wadanda ke yiwa mahukunta a kasar nan gatsali a magana ba, an sha yin hakan ba sau daya ba.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Yadda aka hukunta masan da suka zagi Ganduje a cikin bidiyon barkwanci a Kano

Wannan lamari dai na zuwa ne makwanni kadan bayan da wata kotu a jihar Kano ta umarci a yiwa wasu matasa masu barkwanci bulala 20 kowannensu bisa bata sunan gwamna Ganduje.

An kamo matasan ne tare da gurfanar dasu a gaban kotu bayan da suka yada wani bidiyon barkwanci da suka ambaci sunan gwamnan cikin rashin ladabi.

An tuhume su da laifuka biyu da suka hada da bata suna da kuma yin kalamai masu tada rigima a cikin al’umma.

Bayan sauraran karar, Aminu Gabari, mai shari’a a kotun ta majistere ya umarci a zane su bulala 20 kowanne kuma su share harabar kotu na tsawon kwanaki 30.

Asali: Legit.ng

Online view pixel