Amarya ta Halaka Uwargidanta da Tabarya a Bauchi a Kan Tsire

Amarya ta Halaka Uwargidanta da Tabarya a Bauchi a Kan Tsire

  • Matar aure mai shekaru 20 a kauyen Gar dake Alkaleri ta jihar Bauchi ta halaka kishiyarta ta hanyar buga mata tabarya a kai
  • Mijin matan biyu ya kai rahoto caji ofis inda yace amaryarsa Hafsat ta shiga dakin uwargidansa inda ta buga tabarya a kai tana bacci
  • Wacce tayi kisan ta sanar da ‘yan sanda cewa tsire kishiyarta ta aike mata da shi wanda yasa tayi ciwon ciki da amai, hakan ya wata huce fushi ya

Bauchi - Wata matar aure ta shiga hannun jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi kan zarginta da ake yi da halaka kishiyarta da tabarya.

Matar aure ta halaka kishiyarta
Amarya ta Halaka Uwargidanta da Tabarya a Bauchi a Kan Tsire. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wacce ake zargin ta buge uwargidanta da tabarya a kai wanda yasa ta fadi ta mutu.

Lamarin kamar yadda ‘yan sanda suka sanar, ya faru a kauyen Gar dake gundumar Pali a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Machina Matsayin ‘dan Takarar Yobe ta Arewa

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Walil, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai yace mijin wacce ake zargin ne ya kai rahoton lamarin zuwa hedkwatar ‘yan sanda dake Maina-Maji a ranar 22 ga watan Nuwamban 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakil, ‘dan sanda mai mukamin sufiritandan yace:

“A ranar 22 ga watan Nuwamban 2022 wurin karfe 6 na yamma, wani Ibrahim Sambo mai shekaru 40 daga kauyen Gar ya je hedkwatar ‘yan sanda tare da kai rahoton cewa a ranar matarsa Maryam Ibrahim mai shekaru 20 ta shiga dakin uwargidanta Hafsat Ibrahim mai shekaru 32 inda ta masgeta da tabarya a kai.
“A sakamakon hakan, uwargidan ta samu miyagun raunika kuma an kai ta dakin shan magani dake kauyen Gar inda aka tabbatar da mutuwarta.
“Bayan samun rahoton, tawagar masu bincike dake aiki da rundunar sun hanzarta fadawa aiki tare da damko wacce ake zargin.”

Kara karanta wannan

Kaddara Ta Riga Fata: Kyakkyawar Budurwa Ta Kaso Aurenta Bayan Watanni 3, Ta Wallafa Hotunan Shagalin Bikin, Jama’a Sun Yi Martani

“Yayin tuhuma, wacce ake zargin ta amsa cewa ta aikata laifin. Tace a ranar Talata wurin karfe 12 na safe marigayiyar ta aiko ‘dan ta da tsire ya kawo mata wanda ya sanya ta ciwon ciki da amai bayan ta gama.
“Bayan nan, wacce ake zargin ta kira matar kanin mijinsu tare da bata labari. Ta kara da cewa Faiza tace mata ciwon m ciki ne inda ta bata magani.
“Daga bisani cike da fushi wacce ake zargin ta shiga madafi tare da dauko tabarya ta shiga dakin uwargidan yayin da take bacci ta buga mata a kai wanda hakan ya kawo mutuwarta.”

- Takardar ta kara da cewa.

Matar aure ta halaka miji kan zai yi mata kishiya

A wani labari na daban, wata mata mai suna Salamatu Shehu dake zama a garin Ragin Gero na karamar hukumar Anka a Zamfara ta halaka mijinta.

An gano cewa mijin yana tsaka da shirin yi mata kishiya ne saboda hakan ta halaka shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel