Abun da Ciwo: Kyakkyawar Budurwa Ta Kashe Aurenta Na Watanni 3, Ta Saki Hotunan Bikinta

Abun da Ciwo: Kyakkyawar Budurwa Ta Kashe Aurenta Na Watanni 3, Ta Saki Hotunan Bikinta

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don sanar da mutuwar aurenta watanni uku bayan ta amarce
  • Matar wacce ta ke cike da nauyin zuciya ta wallafa hotunan shagulgulan bikin aurensu dauke da wasu sakonni
  • A cewarta, daukar juna biyu yayin soyayya bai isa dalili da zai sa ka auri mutumin ba

Wata matashiyar ‘yar Najeriya mai suna Bolaghold ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa aurenta na watanni uku ya mutu murus.

Da take wallafa hotunan shagulgulan aurenta a TikTok, Bolaghold ta tabbatar da ganin cewa ta rufe fuskar mijin nata da alamar kuka a kai.

Mata da miji
Abun da Ciwo: Kyakkyawar Budurwa Ta Kashe Aurenta Na Watanni 3, Ta Saki Hotunan Bikinta Hoto: TikTok/@bolaghold
Asali: UGC

A wani wallafa da ya biyo baya, Bolaghold ta rubuta cewa matsaloli biyu ba za su taba haifar da daidai ba.

Ta rubuta a bidiyon cewa samun juna biyu baya nufin dole sai masoya biyu sun auri junansu.

Kara karanta wannan

Da Gaske Akwai Maganar Aure Tsakanin Darakta Mustapha Waye Da Hajara Izzar So Kafin Rasuwarsa? Jarumar Ta Fayyace Gaskiyar Lamari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sashin sharhi, ta yiwa jama’a alkawarin sanar dasu musababbin rabuwarsu da mijinta nan gaba kadan.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama’a sun yi martani

Omolara ta ce:

“Nagode Allah ba’a bari na haifi uban dana ba shekaru 14 da suka wuce, koda dai na makance a soyayya, bayan na haihu sai ya sauya gaba daya, yanzu Allah ya albarkace ni.”

user3047683783435 ya ce:

“Na dauki cikin wannan gayen sannan aka tilasta mun aurensa amma nace sam ba dani ba. A takaice na yi barin cikin sannan ya nuna mun halinsa na gaskiya.

Mhlanga85 ya ce:

“Me ya faru Allah bai albarkace ki da auren wata uku ba a zahirin gaskiya baya son saki sai dai idan kin shigo da wani mutum na daban tsakaninki da mijinki.”

Elo Imma ya ce:

Kara karanta wannan

Hotuna Daga Shagalin Bikin Jarumar Kannywood, Halima Atete, Jama'a Sun Yi Martani

“Ki yi hakuri ‘yar uwa ya fi da ace akwai ‘ya’ya a tsakanin, duniya zata turo maki abokin rayuwarki ki zuba ido.”

Abimbola Adedotun Ad ta ce:

“Lokaci mafi wahala a aure shine watanni 12 na farko.”

Maza guduna suke saboda lalaurata, Budurwa ta koka

A wani labarin, wata budurwa ta je soshiyal midiya don kokawa kan yadda samari ke gudunta saboda lalurar da take da shi.

Budurwa wacce ta kasance kurma ta ce idan gaye ya fito ya nuna yana sonta da ya gano ita din kurma ce sai ya ari na kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel