Hukumar DSS Ta Musanta Janye Tuhumar da Take Wa Tukur Mamu a Kotu

Hukumar DSS Ta Musanta Janye Tuhumar da Take Wa Tukur Mamu a Kotu

  • Hukumar tsaro DSS ta musanta labarin da ake yaɗawa cewa ta janye ƙarar da ta shigar Gaban Kotun tarayya kan Tukur Mamu
  • Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya bayyana labarin da wanda ya sauka kan hanya inda yace shari'a bata ƙare ba
  • Jami'an tsaro sun yi ram da tsohon mai shiga tsakani da 'yan ta'adda Mamu ne a ƙasar Masar sa'ilin yana tare da iyalinsa

Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta rahoton da ke yawo cewa ta janye ƙarar data shigar da Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakani da 'yan ta'adda.

Wani rahoton da ake yaɗawa ya yi ikirarin cewa hukumar ta janye ƙarar da ta shigar a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, inda ta samu sahalewar tsare shi na kwana 60.

Tukur Mamu.
Hukumar DSS Ta Musanta Janye Tuhumar da Take Wa Tukur Mamu a Kotu Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Rahoton ya nuna Lauyan DSS, A. M Danlami ya shaida wa Mai shari'a Nkeonye Maha, jim kaɗan bayan kiran ƙarar, cewa hukumar ta jingine shari'ar.

Menene gaskiyar lamarin?

Amma a wata hira da jaridar Daily Trust ranar Alhamis da daddare, mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana rahoton da, "Karya mara tushe."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Afunanya ya jaddada cewa DSS ba ta janye ko tuhuma ɗaya da take wa Tukur Mamu ba, inda ya bayyana cewa lamarin wani batu ne da za'a cigaba da shi.

Idan baku manta ba a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, Jami'an tsaro suka kama Mamu a Cairo, babban birnin ƙasar Masar lokacin yana tare da iyalansa.

Mamu, fitaccen ɗan jarida a Kaduna kuma makusancin Shahararren Malamin Nan, Sheikh Ahmad Gumi, shi ya shiga tsakanin FG da 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da Fasinjojin jirgin ƙasa.

Bugu da kari, Mamu ya yi nasarar kubutar da wasu daga cikin Fasinjojin amma daga bisani yace ya tsame hannunsa daga lamarin saboda wasu dalilai, vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma Ministan harkokin cikin gida yace gwamnatin tarayya ta gama bincice kan fashin gidan yarin Kuje, Abuja

Ogbeni Rauf Aregbesola, yace an gama binciken amma sakamakon ya shafi tsaro ba za'a bayyana wa duniya ba.

Haka zalika Ministan yace gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta yi abin a zo a gani yadda ta murkushe ƙungiyar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel